VoA Hausa —
Gungun maharan dauke da bindigogin AK-47 sun kai samame ne a makarantar sakandaren gwamnati ta koyar da kimiya a gundumar Kankara da misalin karfe 9 da minti 40 na yamma a shekaranjiya Juma’a, a cewar ‘yan sandan yankin.
Iyaye da ma’aikatan makarantar sun fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa a cikin dalibai 800 ba a gano kimanin rabin su ba.
Wata sanarwa daga shugaba Muhammadu Buahri ta ce sojojin sun gano inda aka yi garjuwa da daliban a cikin jeji kana sun yi musayar wuta da su da taimakon jiragen yaki.
A cikin sanarwar, shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kai a jihar sa ta asali. ‘Yan sanda da sojoji na aiki domin tantance mutum nawa aka yi garkuwa dasu kana nawa suka bata.
‘Yan sanda da suka isa inda aka kai harin a ranar Juma’a sun yi musayar wuta da maharan, lamarin da ya ba wasu daliban damar arcewa, inji mai magana da yawun ‘yan sandan Gambo Isah a cikin wata sanarwa.
‘Yan sanda sun dauki karin jami’ai domin nema da ceto daliban. Wani jami’in dan sanda guda ya samu rauni a musayar wuta da maharan,a cewar su.
Katsina ta fada cikin rashin zaman lafiya da gwamnatin jihar take alakantawa da ayyukan ‘yan bata gari dake kai hare hare a kan al’ummar jihar suna garkuwa dasu domin karbar kudin fansa.
An dai saba ganin hare haren mayakan ‘yan bindiga masu ikirarin yakin musulunci ne a arewa maso gabashin kasar.