Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake gabatar da sunan Farfesa Mahmood Yakubu, a majalisa domin sake ci gaba da jagorantar hukumar zabe a wa’adi na biyu.
Shugaba Buhari ya tabbatar da sake naɗa Farfesa Yakubu ne a cikin wata wasika da ya aika wa shugaban majalisar dattiajai Sanata Ahmed Lawan, kamar yadda mai magana da yawunsa Femi Adesina ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Shugaban ya ce “bisa tanadin sashi na 154 (1) na kundin tsarin mulki na 1999 (Wanda aka yi wa kwaskwarima). Ina farin cikin gabatar da Farfesa Mahmood Yakubu ga majalisa domin tabbatar da shi a matsayin Shugaban, Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) a karo na biyu kuma wa’adi na ƙarshe. “
(BBC Hausa)