Ba zan fasa ɗaure duk wanda aka kama da cin hanci ba, inji Buhari

SHUGABA BUHARI
Hakkin mallakar hoto
BUHARI SALLAU

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa har yanzu yana kan bakansa cewa duk wanda aka kama da laifin cin hanci sai ya sha dauri.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ya ambato Shugaba Buhari yana bayyana haka a sakon da ya fitar na cikar shekara biyar tun da ya soma mulkin kasar.
Shugaban na Najeriya ya zayyana bangarori uku wadanda ya ce su ne manyan batutuwan da ya fi mayar da hankali a kansu.
“A game da yaki da cin hanci, babu wani shafaffe da mai. Idan ya aikata laifi, za ka yi zaman gidan yari. Babu gudu, babu ja da baya,” a cewar shugaban kasar.
Shugaba Buhari ya kuma jero irin nasarorin da ya ce ya samu a yaki da mtasalolin tsaro da suka addabi kasar yana mai cewa a baya matsalolin sun ci karfin Najeriya amma yanzu an samu sauyi sosai.
“A watan Mayun 2015, matsalar tsaro ta addabi ko ina a kasar nan. Babu wanda ya yi tsammani kasar za ta kai wata daya, ba ma shekara daya ba. Baba-bamai sun yi ta tashi kamar abin wasan yara, ‘yan ta’adda sun mamaye kasar, sannan masu aikata wasu laifukan sun yi kamari. Rayuwa ta tabarbare.
A cikin shekara biyar, mun farmaki ‘yan ta’adda da masu tayar da baya har inda suke. Kuma kullum ana kakkabe su, inda ake kusa da kawar da su baki daya,” a cewarsa.
Shugaba Buhari ya ce ya samu nasarori wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, yana mai cewa yanzu an daina dogaro da man fetur kadai.
“An bunkasa aikin gona, an samu ci gaban masana’antu, sannan ma’adinai suna taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki. Kasar nan tana dab da zama mai dogaro da kanta wajen samar da abinci, inda yanzu aka daina shigo da shinkafa da wake da masara da gero da dukkan hatsi,” in ji Shugaba Buhari.
Sai dai duk da wadannan nasarori da shugaban na Najeriya yake ikirarin samu, masu lura da lamura na ganin al’amura sun tabarbare, suna masu cewa akwai bukatar gwamnati ta zage damtse wajen sauya rayuwar ‘yan kasar.

Related Articles