Sheikh Jingir ya sauya matsayinsa kan coronavirus

Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir

Hakkin mallakar hoto
Facebook/Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir

Image caption

Shaikh Jingir ya ce zai yi biyayya ga hukumomin Najeriya

Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, malamin addinin Musuluncin nan na garin Jos a arewa ta tsakiyar Najeriya, wanda ya ce coronavirus ba gaskiya ba ce, yanzu ya ce tabbas cutar gaskiya ce.

Wata sanarwa da Shiekh Nasiru AbdulMuhyi, shugaban gudanarwa na kasa na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a wa ikamatus Sunnah ya aike wa manema labarai ranar Litinin, ta ce za ta yi biyayya ga dukkan dokokin da gwamnatin tarayya da na jihohi suka sanar domin dakile yaduwar coronavirus.

“Kwamitin Koli na kasa na JIBWIS a karkashin jagorancin Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya sanar da bin dukkan umarni na harkokin lafiya da zamantakewa da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi suka dauka domin yakar COVID-19 a Najeriya.

“Domin nuna cewa tana goyon bayan wanan umarni, kungiyar ta dauki matakan kare lafiya, wadanda suka hada da samar da man goge hannu na hand sanitizer a ofisoshi da wuraren ibada, bai wa juna tazara da kuma rufe dukkan makarantun rainon yara da firamare da makarantun gaba da sakandare inda dalibai fiye da miliyan bakwai ke karatu a duk fadin Najeriya,” in ji sanarwar.

Kazalika kungiyar ta dakatar da tarukan karatun Qur’ani na alkalai da malamai da sauran masu alkalanci, in ji sanarwar.

A baya dai Ash-Sheikh Jingir a wani bidiyo ya soki matakan da gwamnati ta dauka na hana Sallar Juma’a da ma rufe Ka’abah da Saudiyya ta yi, yana mai cewa Yahudawa ne suka kirkiro coronavirus domin hana Musulmai aikin Hajji.

Daga bisani, Malamin ya sake yin hira da ‘yan jarida inda ya soki matakin, sannan ya ce babu wanda ya isa ya hana su halartar sallah cikin jam’i. Lamarin dai ya jawo masa suka daga bangarori da dama inda wasu malaman suka bukaci Musulmai su yi watsi da kalaman malamin.

More from this stream

Recomended