Tsohon gwamnan Jihra Abia, Orji Kalu (Hoto: Shafinsa na Twitter)
Photo: Twitter
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan da ta same shi da laifin yin almundahanar Naira biliyan 7.2 da kuma halalta kudaden haram.
Yayin zaman kotun a yau Alhamis, kamar yadda rahotanni daga Najeriya suka ruwaito, Alkali Muhamamd Idris, ya yanke wa Kalu wanda Sanata ne mai ci, hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekara 12.
Gabanin yanke hukuncin, Alkalin ya ce, Kalu ya ci amanar da aka damka masa a jihar.
Tsohon gwamnan na da damar daukaka kara, amma an ba da umurnin a kai shi gidan yari.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ce ta gabatar da tuhume-tuhume 39 akan Kalu tare da tsohon kwamishinan kudi na jihar ta Abia, Jones Udeogo da kuma kamfaninsa mai suna Slok Nig.
Kotun, ta yankewa Udeogo hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10 kana ta ba da umurnin a rufe kamfanin.
Tun dai daga shekarar 2007 aka fara sauraren karar ta Sanata kalu, jim kadan bayan da ya bar ofisi a matsayin gwaman jihar ta Abia.