Me ya sa ‘yan Isra’ila ke zama a yankunan Falasdinawa? | BBC Hausa

Wata mace da 'ya'yanta a wajen matsugunin wucin gadi

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Dubun-dubatar Yadudawa ne ke zaune a Yammacin Kogin Jordan

Shekara da shekaru zaman da Yahudawa ‘yan kama wuri zauna ke yi a mazaunin Falasdinawa misali gabar kogin Jordan da gabashin birnin Kudus shi ne babban abin da ke haddasa tashin hankali tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Kasashen duniya dai na kallon zaman a haramtacce da ya sabawa doka, bai kuma kamata Isra’ila ta daure wa ‘yan kasarta gindin zama a wurin ba a lokacin yakin da aka yi na kwanaki shida a shekarar 1967.

Amurka na cikin kasashen da ba su amince da zamansu ba, kuma a ko da yaushe suna fadin hakan, amma a ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba 2019 ta sauya batun.

Sakataren harkokin wajen Amurkar Mike Pompeo, shi ya sanar da cewa daga wannan ranar gwamnatin kasarsa ba za ta kara kallon zaman da Yaduwan ke yi a Yammacin Kogin Jordan da haramtacce ba.

“Maganar cewa gine-ginen da farar hula suka yi a Yammacin Kogin Jordan ya sabawa dokokin kasa da kasa ba haka ba ne, kuma babu wata kafar ungulun da yake yi wa zaman lafiyar yankin,” inji Pompeo.

Hukumomin Falasdinu sun ce wannan yanki mallakinsu, kuma suna fatan su shiga cikin tsarin sabuwar kasar nan gaba.

Don haka sun yi watsi da sanarwar Amurka kan halaccin zaman Yahudawa, tare da cewa sanarwar barazana ce ga zaman lafiyar duniya baki daya, da kuma yi wa dokokin kasa da kasa karan-tsaye.

Firai Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya yi watsi da hakan, tare da kira ga kasashen duniya su ma su dauki mataki irin nasa.

Kamar yadda wakiliyar BBC a yankin Gabas Ta Tsakiya Barbara Plett-Usher ta ruwaito cewa, matakin ba kawai zai lalata shirin da aka fara na zaman lafiya mai dorewa a yankin ba, hakan zai shafi Falasdinu a matsayin kasa da ‘yancinta, zai kuma kara wa Yaduwa kwarin gwiwar sake mamaye yankin.

Anan muna son kawo wasu tambayouyi da amsarsu don fahimtar yadda rikici tsakanin Falasdinu da Isra’ila ya ke.

Ina ne Isra’ila ta mamaye?

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Benyamin Netanyahu ya sha alwashin ba zai kara cire matsugunan yahudawa ba

Gidajen da ake ginawa dai ana yin su ne a wurin da Isra’ila ta yi kwacensu karfi da yaji a lokacin yakin da aka yi a yankin Gabas Ta Tsakiya a shekarar 1967.

Wadannan wurare sun hada da Yammacin Kogin Jordan, da gabashin Birnin Kudus wanda a baya Jordan ta mamaya, sai kuma Tuddan Golan da ke wani bangare na kasar Syria.

Yawancin Yahudawa sun koma zama a yankunan saboda dalilai na addini, sun yi amanna Ubangiji ne da kansa ya bai wa Yahudawa wannan wuri don su zauna.

Wasu kuma sun koma wajen ne saboda arhar da gidaje suke da su anan.

A ina su ke?

Kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan mazaunan Yahudawa da tabbatar da zaman lafiya ta tabbatar, akwai matsugunai 132, da matsugunan wucin gadi 113 da aka gina ba tare da izinin hukuma ba a Yammacin Kogin Jordan.

Kungiyar ta ce sama da mutum 413,000 ne ke zaune a yankin, kuma suna karuwa a kowacce shekara.

Haka kuma akwai wasu matsugunai 13 a gabashin Birnin Kudus, inda mutum kusan 215,000 ke zaune.

Haka kuma Isra’ila ta sake mamaye wani bangare na Zirin Gaza da ke yankin Sinai na kasar Masar duk dai a shekarar 1967, amma daga baya ta janye.

Sannan akwai wasu matsugunan a yankin Tuddan Golan, su ma da Isra’ila ta mamaye daga hannun Syria a shekarar 1967 lokacin yakin Gabas Ta Tsakiya.

Wannan gine-gine sun mamaye kusan kashi 2 na Yammacin Kogin Jordan, amma masu suka na ganin filaye da gonakin da ke yankin da hanyoyi, kamata ya yi a ce sojoji ne ke tafiyar da tsaronsu.


Me ya sa batun matsugunan ya zama a gaba a tsakanin kasashen?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wata Bafalasdiniya tana yi wa wata sojar Isra’ila ihu a lokacin zanga-zanga

Babbar tambayar da ake yawan tambaya ita ce me ake yi da matsugunan, kuma me ya sa ta zamo sahun gaba idan ana batun rashin zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isara’ila, da ganin yana taka rawa wajen gurgunta tattaunawar zaman lafiya da akai yunkurin yi a lokuta da dama.

Mamayar da matsugunan ba su ne matsalar Falasdinu ba, matsalar ita ce ‘yancinsu da aka take da takura su da ake yi wajen kafa daruruwan shingayen binciken ababen hawa, wadnda sojoji da jami’an tsaron Isra’ila ke amfani da damar wajen cin zarafinsu.

Akwai wata tambayar daban: Falasdinawa sun ce mamayar da Yahudawa suka yi wa Yammacin Kogin Jordan na yi wa fafutukar da suke yi na kara fadada yankin cikin kasarsu kafar ungulu.

Sun kuma bukaci Isra’ila ta dakatar da gine-ginen da ake yi a wajen kafin su amince su koma teburin sulhu.

A nata bangaren, Isra’ilar ta ce Falasdinawa na fakewa da batun don kin halartar zaman sulhun, tare da cewa karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo a shekarar 1993 tsakanin kasashen biyu, batun mazaunan an kai shi karshe ne har sai an cimma yarejeniyar zaman lafiyar.


Me ya sauya matsayar Amurka lokacin mulkin Trump?

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

US President Donald Trump has rarely criticised Israeli settlement activity

Abubuwa da dama sun sauya.

A farkon hawansa shugaban kasa a shekarar 2017, Donald Trump ya nuna cewa yana iya shanye komai ba kamar wanda ya gaji mulki a hannunsa ba, wato Barack Obama.

Kafin Trump ya zama shugaban kasa, Amurka ta sha kiran matsugunan Yaduwan da ba su dace ba amma ba ta taba kiransu ba bisa ka’ida ba tun bayan mulkin Carter a shekarar 1980.

Amma daftarin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na watan Disambar 2016, ya ce ba bu wata shaida a rubuce da ta tabbatar da matsugunan an yi su bisa ka’ida, hakan kuma na janyo tashin hankali da ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kamar sauran kudurorin da aka kafa kan Isra’ila, wadanda ake amfani da su a matsayin haramtattu.

Amma sai ga shi sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a ranar Litinin 18 ga watan Nuwamba 2019, ya bayyana matsayar gwamnatin Shugaba Donald Trump kan halatta matsugunan Yahudawa ‘yan kama wuri zauna da nuna goyon bayan hakan.

Pompeo ya nanata cewa matsugunan ba su sabawa dokokin kasa da kasa kai tsaye ba.

Shi ma Netanyahu ya kara samun kwarin gwiwa fiye da lokutan baya, da fadi da babbar murya cewa ba su aikata ba daidai ba. Ba kuma tare da la’akari da gargadin da Falasdinu ta yi kan gurgunta zaman lafiyar yankinsu ba.


Akwai alamun za a ci gaba da yarjejeniyar?

Alamar hakan mai yiwuwa ce.

Shekara da shekaru Isra’ila tana shirin daukar matakin da zai bakanta tattaunawar zaman lafiyar, daga bisani ta janye daga wuraren da ta fara ginawa tare da cire wasu daga cikin baraguzan ginin da suka fara wanda sojinta suka jagoranta.

Har wa yau gine-ginen da suka yi a yankin Sinai da wasu kananan yankuna hudu a Yammacin Kogin Jordan ma sun cire a shekarar 2005 kafin suka janye.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Isra’ila ta rushe gine-ginen da ta yi a shekarar 2005, kafin ta janye daga yankin baki daya

Yayin da kasashen biyu suka amince su hau teburin sulhu dan sasantawa da samar da zaman lafiya a kasashensu, wannan sabon batun ka iya yin nakasu ga zaman.

Netanyahu ya bayyana kara da shan alwashin ba zai dakatar da sabbin gine-ginen ba, matukar ya dauki matakin hakan na nufin sai an sake sabon zama.

Me dokokin kasa da kasa suka ce kan matsugunan?

Yawancin kasashen duniya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya, da kotun duniya suna daukar matsugunan Yahudawan da ba bisa ka’ida ba.

Wannan na cikin babban taron zaman lafiya da aka yi a Geneva a shekarar 1949, wanda ya haramta irin wannan mamaya.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Majalisar Dinkin Duniya da Isra’ila sun sha hautsinawa kan matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan

Related Articles