
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
A ranar Laraba ne gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar kafa sababbin masarautu guda hudu da suka hada da Rano da Karaye da Gaya da Bichi.
Da saka hannu a wannan sabuwar doka, gwamnatin Jihar Kano za ta nada sababbin sarakuna na wannan masarautun huda da kuma zana iya fadin kasarsu, sannan kuma shi Sarkin Kano na yanzu Muhammadu Sanusi II zai zama Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.
Sai dai ana ci gaba da samun mabanbantan ra’ayoyi daga jama’a daban-daban a fadin Najeriya tun bayan da gwamnatin jihar Kano ta amince da wata doka da majalisar jihar ta sa wa hannu na rarraba masarautar Kano zuwa gida biyar.
A shafin BBC Hausa na Twitter wannan cewa ya yi ”Masarautar Kano masarauta ce mai iko… Kirkirar wasu zai janyo koma bayane ga al’adar bahaushe musamman dan Kano.. Sannan masarautar zata kasance ba ta da iko koh tasiri kuma.”
Wannan kuma na cewa ”Wannan ra’ayin sa ne amma mu muna goyan bayan wannan tsari na kara masarautu a kano.”
”Wannan siyasa ce kawai ba batun yanci ba ..kuma mu dai bamu goyan bayan sa.”
Wannan kuma ya mayar da martani ne ga mai magana na sama inda ya ke cewa ”To ai shi ma Sarki Sanusin siyasa ce ta sa ya zama Sarki, in ban da siyasa da yanzu Sunusi Ado Bayero shi ne Sarki.”
Wasu na ganin wannan rikicin na kasa masarautar gida biyar wani yunkuri ne na rage karfin Sarkin Kano Muhammad Sanusi II wanda ake gani kamar yana yawan sukar manufofin gwamnati.
Amma hukumomi a jihar sun bayyana cewa an kasa masarautar zuwa gida biyar ne domin tabbatar da cewa an kara matso da mutane kusa da sarakuna.
Gwamnatin ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za ta bayar da takardu ga sabbin sarakunan.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za kuma a bayyana ranar da za a nada sabbin sarakunan sarautunsu.
Masarautar Kano ita ce masarauta mafi girma a Najeriya mai kananan hukumomi 44 a karkashinta.
Sai da a yanzu haka sarkin an bar shi da kashi daya cikin biyar na yankunan da yake da iko da su.
Sabbin masarautun sun hada da Rano da Gaya da Karaye da Bichi.
A da hakiman da ke karkashin sabbin masarautun suna karkashin sarkin na Kano ne, amma a yanzu duk mukaminsu daya.
Har yanzu sarkin na Kano Muhammadu Sanusi II, wanda tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne bai ce komai ba kan wannan lamarin.
Yadda tsarin masarautun zai kasance
Sarkin birni da kewaye na da kananan hukumomi 10 a karkashinsa da suka hada da:
- Fagge
- Nassarawa
- Gwale
- Dala
- Tarauni
- Kano Municipal
- Minjibir
- Ungogo
- Kumbotso
- Dawakin Kudu
Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:
- Rano
- Bunkure
- Takai
- Kibiya
- Sumaila
- Doguwa
- Kiru
- Bebeji
- Kura
Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:
- Gaya
- Ajingi
- Albasu
- Wudil
- Garko
- Warawa
- Gezawa
- Gabasawa
Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:
- Gaya
- Ajingi
- Wudil
- Garko
- Gezawa
- Gabasawa
Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:
- Bichi
- Bagwai
- Shanono
- Tsanyawa
- Kunci
- Makoda
- Danbatta
- Dawakin Tofa
- Tofa
Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananan hukumomi kamar haka:
- Karaye
- Rogo
- Gwarzo
- Madobi
- Rimin Gado
- Garun Malam
Wata sanarwa da gwamnatin jihar Kano ta fitar ta ce Sarkin Birnin Kano da Kewaye Muhammadu Sanusi II shi ne zai samu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakinsa.
Sannan shugabancin wannan majalisa zai zama na karba-karba ne inda kowane shugaba zai shekara biyu, inda bayan kammaluwar wa’adinsa sai kuma gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani wa’adin karo na biyu.Sannan sauran ‘yan majalisar masarautun sun hada da:
- Sakataren gwamnatin jiha
- Kwamishinan kananan hukumomi
- Shugabannin kananan hukumomi
- Hakimai masu nada sarki bibbiyu daga kowace masarauta
- Wakilcin mutum biyar da gwamna zai nada.
Sanarwar ta kuma ce: “Sako na karshe kuma shi ne sabuwar dokar bata hana wani wanda ya gaji sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye ba, in dai har sun gada.”