Tsohon Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa ba zai mara wa kowanne ɗan takara daga Arewacin Najeriya baya ba a zaben shugaban ƙasa da za a gudanar a shekarar 2027.
Ortom ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai, inda ya jaddada cewa zai fi son goyon bayan ɗan takarar daga Kudancin ƙasar – ko daga jam’iyyarsa ta PDP ko kuma daga wata jam’iyya dabam – matuƙar yana da cancanta da hangen nesa.
Ya ce akwai yarjejeniya tsakanin yankunan Arewa da Kudu cewa kowanne yanki zai yi wa’adin shekara takwas, kuma hakan bai kamata a karya ba.
Ya kuma ce a 2023 ya zaɓi goyon bayan ɗan kudu a maimakon ya mara wa ɗan takarar arewa baya, har ma da yin asarar kujerarsa ta Sanata.
Ortom ya kuma bayyana cewa ko da kuwa jam’iyyarsa ce za ta tsayar da ɗan takara, ya kamata a fito da wanda ya fito daga Kudancin ƙasar, domin a ci gaba da mutunta tsarin juyawa tsakanin Arewa da Kudu.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi tallafin mai da gyaran haraji. Ya buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’a domin samun shugabanni masu nagarta.
Zaben 2027: Ba Zan Taba Mara Wa Dan Takarar Arewa Ba – Cewar Ortom
