Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa bai da wata sha’awa ko niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
A wata tattaunawa da ya yi da Arise News, El-Rufai ya bayyana cewa abinda kawai yake so a yanzu shi ne ganin an kifar da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wacce ya bayyana da cewa “ta addabi ‘yan Najeriya kuma ta jefa ƙasa cikin masifa”.
El-Rufai, wanda shi ne tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja, ya bayyana cewa zai mara wa kowace jam’iyya baya matuƙar za a iya amfani da ita domin kifar da Tinubu daga kujerarsa.
A cewarsa, “‘Yan Najeriya sun gaji da jam’iyyar APC mai mulki, kuma suna buƙatar wani sahihin zaɓi.” Ya ƙara da cewa, “Mun gudanar da bincike kuma sakamakon ya nuna cewa kaso 91% na al’umma ba sa goyon bayan wannan gwamnati. Wannan shi ne mafi muni a tarihin Najeriya.”
El-Rufai ya ƙara da cewa ya kamata ‘yan Najeriya su haɗa kai su watsar da bambance-bambance da son zuciya domin samar da mafita ga gwamnati mai gazawa.
Da aka tambaye shi ko yana da niyyar yin watsi da son zuciyarsa tare da haɗa kai da manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi, sai ya amsa da cewa, “Ka ambaci sunana, amma ni ban da wata sha’awa. Abinda nake so kawai shi ne in gyara abin da na tarwatsa.”
Ya ci gaba da cewa, “Na taka rawa wajen kafa wannan masifa da aka jefa Najeriya ciki ta hanyar tallafawa fitowar Tinubu a matsayin shugaban ƙasa. Don haka yanzu da ina cikin ƙarshen rayuwata — tunda ina da shekaru 65 kuma ina shirin yin ritaya — ina ganin lokaci ne da zan ba da gudunmawa domin kawar da wannan sharri da zai iya hallaka Najeriya idan aka bar shi ba tare da an dakile shi ba.”
El-Rufai dai na daga cikin fitattun ‘yan siyasar da ke shiga shirye-shiryen kafa sabuwar kawance don kifar da gwamnati mai ci a zaɓen 2027, tare da wasu manyan ‘yan siyasa irin su Atiku da Obi.
2027: Ba Na Sha’awar Takarar Shugaban Ƙasa, Amma Ina Son Kawar Da Bala’in Da Na Dasa Wa Ƴan Najeriya—Elrufa’i
