Majalisar dokokin jihar Zamfara na cikin jimami sakamakon rasuwar ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura Namoda ta Kudu, Alhaji Aminu Ibrahim Kasuwar-Daji, wanda ya rasu da safiyar Laraba a cikin barcinsa.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara ta bayyana alhini kan wannan rashi, tana mai bayyana marigayin a matsayin mutum mai gaskiya, tsoron Allah, da jajircewa wajen hidima ga al’umma da mazabarsa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Yusuf Idris, ya fitar, APC ta ce marigayi Kasuwar-Daji ya bar babban gibi wanda ba za a cika cikin sauƙi ba.
Jam’iyyar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Kaura Namoda ta Kudu da kuma daukacin ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara.
An shirya binne marigayin da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin jiya a ƙauyensa na Kasuwar-Daji, cikin ƙaramar hukumar Kaura Namoda.
Allah ya jiƙansa da rahama, ya kuma ba danginsa da abokan aikinsa haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
Ɗan Majalisa a Jihar Zamfara, Aminu Ibrahim Kasuwar-Daji, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
