Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar Delta.

Rahotanni sun tattaro cewa barayin sun gaza a yunkurin sace matar ne a ranar 2 ga Satumba, 2024, a mahadar Okoloba, titin Jakpa, Uvwie, inda masu garkuwa da mutanen suka kashe ‘yan sanda biyu da direban, Mista David Imela, a yayin da lamarin ya faru.  .

Sai dai mai magana da yawun ‘yan sandan, Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin wa manema labarai a ranar Lahadi a Asaba, babban birnin jihar Delta.

Ya ce, “Bayan yunkurin yin garkuwa da matar daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Delta da bai yi nasara ba, inda wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe ‘yan sandan mobal biyu da direban, kwamishinan ‘yan sanda, Olufemi Abaniwonda, nan take ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro ba tare da ɓata lokaci ba.”

Ƴansanda sun kuma ƙwace wasu makamai daga hannun ƴanbindigar.

More from this stream

Recomended