Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da shi a gidansa.

A cewar Zaidu Bala, mashawarci na musamman kan harkokin talabijin da rediyo ga gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, an yi garkuwa da Bala ne tare da iyalansa, amma abin takaici ya mutu sakamakon harbin bindiga bayan da aka garzaya da shi asibitin kula da lafiya da ke Birnin Kebbi.

“Ga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma.  Alhaji Bako Bala ya rasu – Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Zuru,” Zaidu Bala ya sanar a shafinsa na Facebook.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa yana ci gaba da neman karin haske kan lamarin.

Wannan mummunan kisa shi ne na baya bayan nan a cikin jerin tashe-tashen hankula da ake fama da su a yayin da ake ci gaba da samun ‘yan fashi da makami a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin yaki da ta’addanci da rashin tsaro.

More from this stream

Recomended