Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar ‘yan ta’addar Boko Haram 263 da iyalansu da suka mika wuya a Sashen 1 na kasar Kamaru, daga ranar 10 zuwa 17 ga watan Yulin 2024.

Sanarwar da Laftanar Kanar Abdullahi Abubakar, babban jami’in yada labarai na jama’a ya fitar, ta ce “An fara mika wuya ne a ranar 11 ga watan Yulin 2024, lokacin da ‘yan ta’adda 5 suka mika wuya ga dakarun MNJTF a Wulgo da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.   “Bayanan farko sun nuna wadannan mutane sun fito ne daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar hukumar Marte (LGA), Najeriya.

“A wannan rana, Malum Kori Bukar, mai shekaru 50, ya tsere daga maboyar Jibilaram, sannan ya mika kansa ga sojoji.

“Bugu da kari, a ranar 11 ga watan Yuli, ‘yan ta’adda 19 sun mika wuya a kauyen Madaya da ke arewacin kasar Kamaru, sannan wasu 11 sun mika wuya a Wulgo daga maboyarsj Tumbuma cikin rukuni 2.

“Sannan a ranar 12 ga Yuli, 2024, mutane 64 sun mika wuya a Bonderi, Kamaru, ciki har da manya maza 6, mata 20, da yara 38.

“Bugu da ƙari, a ranar 13 ga Yuli, ‘yan ta’adda 27 su ma sun mika wuya.

“Haka wannan lamari ya ci gaba faruwa har a ranar 15 ga Yuli, 2024, tare da wasu mutane 102 da suka mika wuya a Bonderi, Extreme North Cameroon, ciki har da manya maza 20, mata 40, da yara 42.

“Bugu da kari, mutane 5 ne suka mika wuya a Wulgo, inda 2 suka fito daga maboyar Tumbuma, a kudancin tafkin Chadi.  A ranar 16 ga Yuli 2024, karin wasu ‘yan ta’adda 2 sun mika wuya.

“Washegari, 17 ga Yuli, 2024, an ga jimillar ‘yan ta’adda 48 da iyalansu sun mika wuya, wadanda suka hada da manya maza 10, mata 15, da yara 23.

“Bincike na farko ya nuna cewa duk mutanen da suka mika wuya ƴan al’ummun Najeriya ne.

“Saboda haka, an mika su ga sojojin Operation Hadin KaI don ci gaba da daukar mataki.”

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...