Ƴan sanda sun harba tiyagas kan masu zanga-zanga a Fatakwal

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Rivers sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga da suka hallara a garin Fatakwal da safiyar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar, karkashin jagorancin kungiyar Take It Back Movement, sun taru ne a filin Isaac Boro domin nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci da aka yi a jihar.

An ce jami’an tsaro sun mamaye wajen tun karfe tara na safe (9:00am), inda suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

“Babu wanda zai hana mu taruwa a cikin jiharmu, mu ‘yan Rivers ne,” in ji wasu matasa da ke zanga-zanga, kamar yadda tashar Channels TV ta ruwaito.

Sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce ta riga ta shawarci masu zanga-zangar da su soke shirin, saboda dalilai na tsaro.

More from this stream

Recomended