Kudurin neman kasar nan ta koma salom shugabanci irin na Firaminista ya samu karatun farko a majalisar wakilai ta tarayya.
Kudurin da aka gabatar da shi a majalisar ranar Alhamis ya samu goyon bayan yan majalisa 71.
A yanzu haka dai Najeriya na gudanar da mulki ne na shugaba kasa mai cikakken iko.
Banbanci a tsakanin tsarukan biyu shine ya yin da a tsarin shugaban kasa mai cikakken iko mutane ne suke zaben shugaban kasa kai tsaye shi kuwa tsarin firaminista yan majalisar dokoki ne suke zaben Firaminista.
Da sukewa yan jaridu jawabi yan majalisar wakilan su 71 sun ce tsarin firaminista zai taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kasa da kuma cigaba.
Yan majalisar karakashin jagorancin, Kingsley Chinda daga jihar Rivers ya ce bincike ya nuna cewa kasashen da suke bin tsarin mulkin shugaba mai cikakken iko basa samun cigaba na azo a gani idan aka kwatanta da masu mulki irin na firaminista.
A baya dai Najeriya ta gudanar da irin wannan mulkin zamanin jamhuriya ta farko lokacin firaminista Abubakar Tafawa Balewa.