Ƴan banga sun kashe mai garkuwa da mutane a Sokoto

Ƴan banga sun kashe wani mai garkuwa da mutane mai suna Dogo Oro da ake kyautata zaton yana addabar kananan hukumomin Bunza da Kalgo a jihar Kebbi a kauyen Tunga dake unguwar Tilli a karamar hukumar Bunza.

Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Ahmed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Juma’a.

Da yake tsokaci a kan harkokin tsaro, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake bayar da karin haske kan yanayin tsaro a jihar.

Jihar Sokoto dai na daya daga cikin jihohi ln da fama da ta’addancin a Arewa maso Yammacin Najeriya.

More News

Dakarun Najeriya sun cafke wasu ƴan’aiken ƴanbindiga a Kaduna

Sojoji sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da kaiwa 'yan bindiga sakonninsu a kasuwar ƙauyen SCC da ke ƙaramar hukumar Kachia a...

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴanbanga sun sake kawar da wani ƙasurgumin ɗanbindiga

Rahotanni da ke fitowa daga Arewa maso Yammacin Najeriya na nuna cewa an yi nasarar kawar da wani fitaccen dan bindiga a jihar Zamfara,...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...