Wuraren da ake shan tabar shisha a Ghana za su dinga fuskantar hukunci mai tsanani idan har ba su bi dokokin kiyaye lafiya da kasar ta tanadar ba.
Shan tabar Shisha dai ya zama ruwan dare a tsakanin matasa a kasar.
Sai dai akwai sabanin ra’ayi kan cewa tabar shisha ba ta da illa kamar taba sigari.
Amma Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO da Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ghana FDA, ba su yarda da wannan batu ba.
Hukumar ta ce daga yanzu duk mai mashayar da aka kama ana shan shisha a wajen zai fuskanci zaman gidan yari na shekara uku ko a ci shi tarar dala dubu uku, kwatankwacin naira miliyan daya da 80,000 kenan.
Sai dai wannan hukunci zai hau kansu ne kawai idan ba su yi rijistar shishar ba ko kuma idan ba su sanya sanarwar gargadi kan irin hadarin da ke tattare da shanta yake ba.
Yayin shan shisha
Shan wannan taba mai kanshin gaske na kara karbuwa a wurin jama’a a fadin duniya, amma masana harkar lafiya sun ce mafi yawan wadanda suke shanta ba su san hadarin da ke tattare da hakan ba.
Yanzu dai mutane ne da dama suke cin moriyar wannan taba wadda ke tashe a Indiya da Gabas ta tsakiya inda aka ce daga nan ta samo asali.
A Gabas ta tsakiya yayin ya ratsa har tsakanin ‘yan yara maza da mata da ma manyan mata wadanda yawancinsu ba sa shan taba.
Wannan yayi yanzu ya kai har ga kasashen Turai da Brazil da kuma Amurka inda za ka ga shagunan shan wannan taba mai zamani.