Zaben 2019: Shin da wane yatsa mutum zai dangwala kuri’a?

Za a iya dangwala kuri'a da ko wane yatsa

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a iya dangwala kuri’a da ko wane yatsa

Batun yatsan da mutane ya kamata su yi amfani da shi domin dangwala kuri’arsu a lokacin zabe na neman ya kawo rudani a Najeriya.

Wani sako da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta musamman WhatsApp ya bayyana cewa hukumar zabe ta canza tsarin yadda mutane za su jefa kuri’a.

Cikin bayanin da ake yada wa har da yatsan da hukumar ta ce za a yi amfani da shi.

Amma Hukumar INEC ta karyata labarin inda ta ce masu zabe za su iya amfani da kowane yatsa yayin dangwala kuri’arsu.

A wani bayani da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar zabe ta bayyana cewa masu zabe za su iya amfani da kowane irin yatsa su dangwala kuri’arsu.

“Mai kada kuri’a zai iya amfani da kowanne yatsa domin kada kuri’arsa. Amma ya tabbatar da cewa tawadarsa tana cikin zagayen akwatin jam’iyyar da ya dangwala wa, kada ta shiga cikin akwatin wata jam’iyyar daban,” in ji INEC.

Saboda haka wannan labarin kanzon-kurege ne da wasu ‘yan ta-da-zaune-tsaye suke yadawa.

Sakon karya da ake yada wa

Sakon ya kunshi cewa “a yanzu ba za ka dangwala kuri’a da babban yatsa ba sai dai da dan ali wato manuniya.

“Duk kuri’ar da aka kada da babbar yatsa za a soke ta. Tambayar a nan ita ce, me ya sa ba a wayar da kan ‘yan kasa ba har sai yanzu?

“Me yasa INEC ta boye irin wadannan bayanai masu amfani har sai kwana kadan kafin zabe?

“Don Allah ba wai karantawa kawai za ku yi ba ku tura wa sabbin masu kada kuri’a don su fadaka.

“makomar kasarmu ta dogara ne a kan yatsan dan ali wato (‘yar manuniya)”, in ji sakon.

Sai dai babu wata hujja da ke tabbatar da sahihancin sakon, domin kuwa hukumar zabe ta yi bayani akasin hakan.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...