Za’a Sake Zaben shugaban kasa a wasu jihohi guda uku- INEC

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, wato INEC, ta tabbatar da cewa ta zabi ranar 9 ga watan Maris matsayin ranar sake gudanar da zaben shugaban kasa a wasu wuraren da aka samu matsala a ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Kwamishanan labarai na hukumar INEC, Festus Okoye, ya bayyana cewa za’a gudanar da zaben ne tare da zaben gwamnoni da majalisar dokokin tarayya.

Okoye ya ce an yanke wannan shawara ne bayan ganawar hukumar da wakilan INEC dake jihohin tarayya a ranar Alhamis, 28 ga watan Febrairu, 2019.

INEC ta yi watsi da zaben wasu wurare sakamakon rikice-rikice wanda ya hana hukumar aika kayan zabe da ma’aikata wajen domin kare rayukansu.

Wadannan wurare sun kunshi kananan hukumomi biyu a jihar Ribas,da wasu a jihar Legas da jihar Anambara.

Jawabin yace: ” Saboda haka, hukumar ta yanke shawara cewa za’a gudanar da zaben a dukkan wuraren da ba’a samu damar gudanar da zabe ba a ranan Asabar, 9 ga watan Maris tare da zaben gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha,”.

Idan Za ku tuna cewa rikice-rikice a unguwar Okota dake jihar Legas ya sanadiyyar INEC tayi watsi da sakamakon zaben wajen, kana kashe-kashe da aka yi a jihar Ribas inda akalla mutane 20 suka rasa rayukansu ranar zabe.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...