Zaɓaɓɓen Gwamnan Sokoto Ya Ƙaryata Batun Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Gwamnatin Tambuwal

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya musalta kafa kwamitin da zai binciki gwamna mai barin gado, Aminu Waziri Tambuwal.

Bayanin haka na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Bawa mai magana da yawun zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar a ranar Alhamis.

A cikin sanarwar zaɓaɓɓen gwamnan ya bayyana cewa baki ɗayan labarin kirkirarre ne babu kanshin gaskiya a ciki

Sanarwar ta kara da cewa a iya sanin gwamnan an kafa kwamiti ne na karɓar mulki da zai aiki tare da kwamitin mika mulki da gwamnatin jihar ta kafa.

Zaɓaɓɓen gwamnan ya ƙara da cewa har yanzu bai karbi ragamar jagorancin mulkin jihar ba ballantana ya kafa kwamitin bincike.

More from this stream

Recomended