Yaushe kotu za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano? | BBC Hausa

Abba Kabir Yusuf
Image caption

Abba Kabir Yusuf yana kalubalantar nasarar Gwamna Ganduje

A ranar Alhamis ne kotun mai sauraron kararrakin zaben gwamna ta fara zaman share-fage a kan karar da ke gabanta.

Abba Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba gida-gida”, ya sha kayi a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba.

Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe suka musanta.

Kotun dai tana da kwana 180 ne ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar. A ranar 11 ga watan Afrilun 2019 ne Abba ya shigar da karar.

Ke nan kwanaki 97 ya rage ita wannan kotu ta kammala shari’ar domin yanke hukunci.

Zaman kotun na ranar Alhamis wanda mai shari’a Halima Shamaki ke jagoranta, ya mayar da hankali ne kan tantance bayanai da korafe-korafen da bangaren masu kara da na masu kare kai suka gabatar.

An dai tabka muhawara a tsakanin lauyoyin, inda kowane bangare ya nemi da a kori karar da daya bangaren ya shigar kafin daga bisani kotu ta cimma matsayar dage zaman.

Lauyoyin da ke kare Gwamna Ganduje sun nemi a dage sauraron karar, tare da ba su isasshen lokaci domin su yi nazarin wata sabuwar bukatar da masu kara suka gabatar.

Su ma masu gabatar da karar sun ki amincewa da ita, sakamakon zargin da suke yi cewa lauyoyin da ke kariya na fitar da salo ne kawai na ba ta lokaci.

Dan takarar gwamna na jam`iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf da kuma jam`iyyarsa ne suka shigar da karar bisa zargin cewa zaben cike yake da magudi da kuma aika-aikar `yan bangar siyasa.

Haka kuma masu karar sun bukaci kotu ta yi watsi da sakamakon zaben da aka yi, zagaye na biyu, wanda aka fi sani da “Inconclusive,” bisa zargin cewa babu tsarin Inconclusive a cikin dokar zabe.

Abba Kabir Yusuf da kuma jam`iyyarsa na karar Hukumar Zabe ta Kasa, INEC da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, amma sun musanta zarge-zargen na PDP.

Yanzu dai kotun ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 13 ga wannan watan na Yuli, don ci gaba da shari’ar.

Image caption

Hukumar zabe ta bayyana Gwamna Ganduje da wanda ya lashe zaben da aka yi a watan Maris

  • Kawunan masana shari’a ya rabu kan zaben Kano
  • Duk wanda ya ci zaben Kano a ba shi kawai – Bashir Tofa

Yaushe za a kammala shari’ar?

Barrister Audu Bulama Bukarti ya yi wa BBC bayanin abubuwan da za su faru daga ranar 13 ga watan Yuli idan kotu ta koma zamanta kamar haka:

  • Masu kara za su gabatar da shaidunsu
  • Daga nan kuma sai a bai wa wadanda ake kara su ma su gabatar da nasu shaidun
  • Kotun za ta saurari abin da ake kira jawaban karshe, inda wadanda ake kara za su fara jawabin karshen
  • Daga nan ne kuma sai a bai wa bangaren masu kara su gabatar da nasu jawabin na karshe
  • Kotun za ta sake bai wa wadanda ake kara damar mayar da martani kan jawabin karshe da masu kara suka yi
  • Bayan sauraron jawaban karshe da martani sai kotu ta sa ranar yanke hukunci.

Daya daga cikin hukunci uku da kotu za ta iya yankewa

  • Kotu za ta iya korar karar da Abba Kabir Yusuf, inda za ta tabbatar da Gwamna Ganduje da cin zabe
  • Kotu za ta iya ayyana Abba Kabir Yusuf da wanda ya ci zabe
  • Kotun za ta iya soke zaben domin a sake

Idan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke bai gamsar da daya daga cikin bangarorin ba, sai su garzaya kotun daukaka kara.

Yaushe za a yanke hukunci?

Ita dai wannan kotun ta sauraron kararrakin zaben na da kwanaki 180 ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar.

Kotun Daukaka Kara na da kwana 60 ta yanke hukunci, inda ita ma Kotun Koli take da kwanakin 60 ta yanke nata hukuncin.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...