Yau take ranar mata ta duniya

Masu rajin kare hakkin mata sun ce akwai jan aiki kafin a samu daidaiton
Image caption

A yau ake bikin ranar mata ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a kowacce shekara. Taken bikin bana shi ne daidaita gudunmuwar maza da mata ga cigaban kasa, sai dai ana korafin har yanzu an yiwa mata nisa ta fannoni daban-daban na rayuwa.

Sai dai a yayin da ake wannan bikin, a Najeriya, sakamakon zaben Majalisar dokokin tarayya da aka yi a watan daya gabata ya nuna cewa Mata 6 ne kacal suka yi nasara a Majalisar datawa mai mambobi 109 ya yinda 11 ne suka yi nasara a majalisar wakilai mai mambobi 360.

Tuni dai wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin mata suka fara bayyana damuwarsu akan sakamakon zaben. Hajiya Saudatu Mahadi ta kungiyar WRAPA ta ce da irin wannan kadai aka kalla za a gane akwai jan aiki a gaba wajen tabbatar da daidaiton da ake son yi tsakanin mata da mata.

Wasu kasashen duniya sun dauki haramin a bukukuwa da zanga-zanga, da machi, da taruka, da shirya laccoci albarkacin ranar mata ta Duniya.

A kasar Philippines daruruwan mata sun cika tituna a birnin Manila, tare da bayyana rashin jin dadin yadda shugaba Rodrigo Duterte ya maida batun yi wa mata fyade tamkar abin barkwanci.

A Brazil ma kusan irin hakan ce za ta kasance inda dubban mata suka shirya wani taro da za su maida martani kan wasu kalaman batanci da shugaba Jair Bolsonaro ya yi akan matan.

Shagalin na ranar mata a kasar Faransa a kuma fadar Elyseezai sha banban, inda shugaba Emmanuel Macron zai bada lambar yabo ta farko ga ‘yancin mata da aka sanyawa sunan wata ‘yar siyasa Simone Veil da ta kubuta daga kisan gillar da ‘yan Nazi suka yi.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...