Yaran da Sai sun yi nunkaya kafin su je makaranta

Yanda karamin yaro ke nunkaya zuwa makaranta

Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Yanda karamin yaro ke nunkaya zuwa makaranta

Kayi tunanin cewa za ka je makaranta cikin ruwa kana nunkaya, ka saka littafanka cikin leda, kanka a saman ruwa kana mutsu-mutsu.

A kowane lokacin kana kokarin fitar da kanka cikin ruwa domin shakar iska a lokacin da kake nunkayar.

Ga wasu yara a Philippines, wannan shi ne abin da suke yi a kullum, amma wata kungiyar bayar da tallafi tana kokarin samar masu sauki ta hanyar samar masu da kwale-kwale.

Kungiyar tallafi ta “Yellow boats” dai ta fara aiki ne a kafafen sada zumunta, kuma bayan ‘yan shekaru kadan ta bunkasa zuwa kungiyar da ke ba da tallafi a fadin duniya.

Ta fara bayar da tallafi ne a wani kauye da mafi yawan al’ummarsa masunta da manoma ne da ke rayuwa a gabar tekun Zamboanga.

Hakkin mallakar hoto
Yellow Boat of Hope Foundation

Image caption

Yara cikin kwale-kwale a hanyar su ta zuwa makaranta

Yaran kauyen kan tuka kwale-kwale na kusan kilomita daya kafin su isa makaranta, idan kuma ruwa yayi yawa, sai tukin kwale-kwalen ya zama nunkaya.

Amma Jay Jaboneta wanda shine ya kirkiri kungiyar tallafin – ya bayyana hakan a matsayin babban hadari ko da kuwa yaran sun iya nunkaya sosai – kuma mafi yawancinsu basu kware ba.

Yaran kan nade kayan makarantarsu da littafansu cikin leda domin gudun jikewa a lokacin da suke hanyarsu ta makarantar.

Mista Jaboneta ya bayyana cewa “ban san haka ne halin da yaran nan suke ciki ba – na girgiza kwarai da naga hakan a Facebook.”

Wannan lamari ya yadu a shafukan sada zumunta musamman bayan da Mista Jaboneta ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin, hakan ya janyo mutane da dama suka fara tara kudi domin taimakawa.

Hakkin mallakar hoto
Facebook

Image caption

Yara tsamo-tsamo cikin ruwa a hanyarsu ta zuwa makaranta

A yanzu haka dai, wannan kungiya tana aiki ne a duk fadin Philippines. Muhimmin aikin da ta ke yi shi ne samar da kwale-kwale.

Kwale-kwalen dai duk an yi masu fentin ruwan dorawa kamar yanda launin motocin kai yara makaranta na kasar suke.

Karamin kwale-kwale ana sayar dashi ne a kan dalar Amurka 200 kuma yakan dauki yara shida zuwa takwas kuma yaran ne za su tuka kwale-kwalen da kansu.

Haka kuma, akwai manyan kwale-kwale masu inji da suke da direba na musamman wanda direban tsohon dalibin makarantar ne ko kuma yana daya daga cikin iyayen yaran makarantar a yanzu.

Hakkin mallakar hoto
Yellow boat of hope foundation

Image caption

Kwale-kwalen launin dorawa ne, tamkar launin motocin kai yara makaranta a kasar.

A yanzu haka dai wannan kungiya ta tallafa wa al’ummomi kusan 200 tun 2010.

Mista Jaboneta ya kuma ce akasari suna aiki ne tare da dattawan gari ko kuma shugabannin makarantu a lokacin da suke bayar da tallafin.

Ya ce: “Da mun samar da kwale-kwale, sai mu bar wa al’ummar da ke wurin su ci gaba da kula ta tafiyar da lamura.”

Hakkin mallakar hoto
Yellow Boat of Hope Foundation

Image caption

Akasarin kananan kwale-kwalen dalibai biyu ne ke iya tuka su

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...