Yara da dama sun makale a ginin bene da ya ruguzo a Lagos

Wani ginin bene mai hawa uku da ke yankin Itaa-Faaji a jihar Lagos ya rushe sannan ya danne yara yan makaranta da dama.

Wani shedan gani da ido ya fadawa jaridar The Cable cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe goma na ranar Laraba. Daya daga cikin hawan benen ana amfani da shi ne a matsayin makaranta kuma yara dalibai na tsaka da karatu lokacin da ginin ya rufta.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos da sauran ma’aikatan ceto na can suna aikin ceto yaran dama sauran mutanen da suka makale.

An garzaya da wasu daga cikin yaran da aka samu nasarar zakulo su daga cikin baraguzan ginin.

Faduwar gini irin haka abune da ya zama ruwan dare a Najeriya kuma da alama hukumomi sun gaza daukar mataki da zai kai ga shawo kan faruwar lamarin.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...