Yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali a garin Bama inda ƙananan yara 33 suka mutu

[ad_1]








Aƙalla ƙananan yara 33 ne suka mutu a sansanin yan gudun hijira dake Bama a jihar Borno sakamakon ƙarancin abinci kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ce ta bayyana haka.

Ƙungiyar ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Garin Bama na daya daga cikin garuruwan da rikicin kungiyar ta Boko Haram ya yi wa muguwar barna da kuma sauran garuruwa dake yankin arewa maso gabas.

“Karancin isasshen taimako, da ya haɗa da makwanci da kiwon lafiya na yin mummunan illa akan kananan yara dake isa garin,”MSF ta bayyana a cikin sanarwar.

“Tun daga watan Afirilun shekarar 2018 sama da mutane 10000 ne suka isa sansanin yan gudun hijira na makarantar sakandaren kimiyya inda muhalli da kuma kula da lafiya basa tafiya kafada da kafada da yawan mutanen da suke karuwa.”

Rahoton ya kara da cewa sama da mutane 6000 ne dake sansanin ke kwana a filin Allah ba tare da kariya daga zafin rana, ruwan sama da kuma sauro.




[ad_2]

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...