‘Yan Bindigar Zamfara Sun Kashe Mutane 13

A wani al’amari mai daure kai, wasu mahara, wadanda wasu ke zargin cewa ‘yan yankin ne, sun sake kai hari a kauyen Gidan Kaso da ke Karamar Hukuma Birnin Magaji ta jahar Zamfara, inda su ka kashe mutane akalla 13 baya ga wadanda su ka ji ma raunuka da kuma dukiyar da au su ka sace au su ka barnata.

Wasu ganau kuma mazauna kauyen na Gidan Kaso, wadanda su ka bukaci a sakaya sunayensu saboda tsoron abin da ka biyo baya, sun ce maharan sun isa garin ne da babura kuma sabe da bindigogi da yammacin jiya Asabar su ka shiga bude wuta da kuma kone-kone. Su ka ce kusan duk wayewar gari sai wadannan maharan sun far ma wasu mutane a yankin. Su ka ce saboda yawan kai hare-haren da mutanen ke yi, har manoman yankin sun kasa zuwa gonakinsu duk kuwa da damina ta kankama.

‘Yan yankin su ka ce idan ma an girke sojoji a Birnin Magaji, kamar yadda hukumomi ke ikirari, to girke sun bai yi wani tasiri ba – a kalla ya zuwa yanzu dai. Haka ma jiragen sintirin da ke tauna tsakuwa a yankin; sun ce bas u hana miyagun cin karansu ba babbaka.

Duk wani kokari na jin ta bakin ‘yan sanda ya ci tura.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...