‘Yan bindiga sun kai hari a jihar Jigawa

Getty Images

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Jigawa ta tabbatar cewa barayi sun halaka mutum daya tare da jikkata wasu mutane, a wani hari da barayin suka kai a garin Maidawa da ke jihar.

Bayanai sun ce maharan sun shiga kauyen ne kan babura, sannan suka je gidan wani attajiri a kauyen suka karbi kudi, suka kuma harbe shi tare da wasu mutanen garin.

Cikin wandanda aka harba har da wasu yara uku kamar yadda aka bayyana.

Duk da cewa ‘yan sanda sun bayyana cewa mutum daya aka kashe, amma mazauna garin na ikirarin kashe mutane da dama a harin da barayin suka kai.

An bayyana cewa barayin sun kai kusan mintuna arba’in suna cin karensu ba babbaka a cikin garin na Maidawa.

Mazauna kauyen sun koka bisa ga faruwar wannan lamarin inda suke ganin kamar irin abubuwan da ke faruwa a wasu wurare sun fara isowa yankin su.

Wasu kuma mazauna garin sun shaida cewa da wayansu ba su taba ganin an kawo hari da bindigogi ba a garin.

Wannan harin da aka kai a Jigawa na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ke kara kamari musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.

Sai dai gwamnatin kasar ta bayyana cewa tana iya bakin kokarinta wajen shawo kan matsalolin.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...