‘Yan bindiga sun bude wa direbobi wuta a Zurmi

Zamfara

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a kan direbobi a titin da ya ratsa karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara zuwa Gurbin-Baure.

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar wani direba guda da kuma sace mutanan da ba a san adadin su ba.

Mazaunan yankin sun shaida wa BBC cewa da Misalin karfe uku da minti biyar na rana, ‘yan bindigar suka tare hanya tare da bude wuta a kan masu wuce wa da kuma kona mota guda.

A cewarsu, kafin jami’an tsaro su isa yankin da abin ya faru ‘yan bindigar sun tsere.

Wannan lamari ya haifar da fargaba tsakanin mazauna yankin da ke zaman dar-dar a yanzu.

Sai dai a yanzu ana iya cewa an dan samu natsuwa sakamakon yadda jami’an tsaro ke kai komo.

An dai kashe daruruwan mutane a Zamfara a tsawon shekara shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.

Hare-haren da barayin shanu da masu satar mutane don kudin fansa ke yi a Zamfara na karuwa, duk da yunkurin jami’an tsaro na kawo karshen ayyukansu.

Gwamnatin jihar ta sha cewa tana daukar mataki domin shawo kan matsalar, ko da yake ana zarginta da hannu a batun amma ta musanta zargin.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...