
Wani mutum ya yanke jikin ya fadi kuma ya mutu nan take lokacin da yake bin layin karɓar katin ATM a wani banki a can jihar Delta.
A cewar jaridar Tribune lamarin ya faru ne a garin Agbor dake jihar Delta.
Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya yanke jiki ya fadi ne bayan da ya shafe a wanni yana bin layin karɓar katin.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar,DSP Bright Edafe ya tabbatar da faruwar.