Wani mai garkuwa da mutane da ya sha Tramadol ya cigaba da bacci kwanaki 6 bayan da aka kama shi

[ad_1]

Rundunar Æ´ansandan jihar Ondo ta bayyana cewa mutumin da ta kama wanda ake zargi da yin garkuwa da mutane na cigaba da sharara bacci kwanaki shida bayan da aka kama shi.

An kama mutumin da ake zargin a ranar Lahadi lokacin da shi da sauran abokan ta’addancinsa suka yi Æ™oÆ™arin yin garkuwa da wata mata dake da shagon sayar da magunguna a Owo dake jihar Ondo.

Ance mutumin ya fita daga hayyacinsa lokacin da suke tsaka da shirin yin garkuwa da matar.

Femi Joseph, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ondo ya ce har ya zuwa yanzu Æ´ansanda sun gaza tatsar wasu bayanai masu muhimmanci a gurinsa.

Joseph ya ce litita ya tabbatar da cewa ya daddaki kwayar Tramadol mai yawa shiyasa yake ta sharara bacci.

Ya kara da cewa an samu 400mg na Tramadol aljihunsa lokacin da aka kama shi.

[ad_2]

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...