Tsokacin masana game da kalaman Buhari a taron ministoci

Fadar shugaban Najeriya ta shirya taron sanin makamar aiki ga sabbin ministoci da shugaban ya nada domin gudanar da gwamnati a zango na biyu.

Yanzu haka masu fashin baki a fannin siyasar Najeriya na tsokaci game da kalaman da shugaban kasar ya yi a lokacin da ya gabatar da jawabi a wurin taron sanin makamar aikin ga asabbin ministocin da ya nada.

Batutuwan da shugaban na Najeriya ya tabo, a wurin taron, sun hada da bitar nasarorin zangon farko na gwamnatinsa da kalubalen yawan jama’a da Najeriya ke fuskanta da mafarkin gwamnatinsa na aza tubalin fitar da matalauta miliyan 100 daga kangin fatara cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban ya kuma tabo batun bukatar da ke akwai ga sabbin ministocin su hada hannu wuri guda ta fuskar tsarawa da aiwatar da manufofin cimma burin gwamnati a ma’aikatun da za su jagoranta.

Sai dai masu kula da lamura sun yi tsokaci game da lafuzzan shugaban.

Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata, shugaban kungiyar CAJA masu rajin tabbatar da adalci kawar da rashawa da kuma alkinta dukiyar kasa, ya ce bayannan shugaban sun saka shakku a zukatan jama’ar kasar.

Ya kuma kara da cewa jawabin nasa ya nuna cewa ita gwamnati ba ta da shirin da za ta kai kasar ga inda ta ce za ta kai ta.

Shi ma masanin kimiyyar siyasa da harkokin dimokaradiya, ya yi tafsili game da kalaman na shugaba Buhari.

Malam Kabiru Sufi, malami ne a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano, ya kuma ce jama’a suna jiran su ga an fitar da wani daftari ko wani babban kudiri da ya wuce wanda aka fitar a halin yanzu.

Yanzu dai ‘yan Najeriya na dakon ganin kamun ludayin sabbin ministocin bayan shugaba Buhari ya tura su ma’aikatun da za su yi wani lokaci a nan gaba.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...