Tsohon gwamnan jihar Gombe Abubakar Hashidu ya rasu

[ad_1]
Toshon gwamnan jihar Gombe, Abubakar Habu Hashidu ya riga mu gidan gaskiya.

Wata majiya daga iyalinsa ta bayyana cewa tsohon gwamnan ya mutu ne da safiyar yau Juma’a a gidansa dake Gombe.

Marigayin ya mutu yana da shekaru 74.

Marigayi Hashidu ya kasance gwamnan jihar Gombe a karkashin jam’iyyar APP tsakanin shekarar 1999 ya zuwa 2003.

Marigayin ya rike mukamai da dama ciki har da ministan albarkatun ruwa da kuma ministan noma da raya karkara.
[ad_2]

More News

An Jikkata Jami’an Tsaro A Harin Da Ƴan Bindiga Su ka Kai Wa Ayarin Motocin Yahaya Bello

A jikkata wasu jami'an tsaro a wani hari da yan bindiga su ka kai kan jerin ayarin motocin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ranar...

Bala Muhammad ya zama shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP

An zaɓi gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP. Siminalayi Fabura zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers shi ne mataimakin shugaban...

Za mu sake bitar mafi karancin albashi a Najeriya—Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin sake nazarin mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan. A cewarsa, akwai bukatar...

EFCC na zargin tsohuwar ministar mata a mulkin Buhari da karkatar da naira biliyan 2

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta titsiye tsohuwar ministar harkokin mata Pauline Tallen kan zargin azurta kai ta...