Babu daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasarnan da suka halarci bikin Ranar Dimakwaradiya da aka gudanar a dandalin Eagle Square dake Abuja.
Taron shine irinsa na farko tun lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimakwaradiya domin girmama marigayi MKO Abiola mutumin da ake tunanin ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993.
Tun a shekarar 1999 da aka dawo mulkin dimakwaradiya ana gabatar da bikin ne ranar 29 ga watan Mayu.
A wannan shekara ma duk da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya karbi rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayu an dage gabatar da wasu bukukuwan ya zuwa ranar 12 ga watan Mayu.
Yayin da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya halarci bikin rantsuwar na ranar 29 ga watan Mayu an gaza ganin fuskarsa a wurin bikin na yau.
Bayan Gowon, tsohon shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar,Olusegun Obasanjo, Gudluck Jonathan, Ibrahim Badamasi Babangida da kuma tsohon shugaban gwamnatin rikon kwarya,Cif Ernest Shonekan dukkaninsu basu halarci wurin taron ba.