Connect with us

Hausa

Trump ya raba gari da jakadan Birtaniya

Published

on

Donald Trump

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Shugaba Trump ya ce Amurka ba ta kaunar jakadan, Sir Kim Darroch, kuma ba zai sake aiki da shi ba

—BBC Hausa

Shugaba Donald Trump ya caccaki gwamnatin Birtaniya da jakadanta a Amurka a matsayin martani na wasu bayanan sirri da jakadan ya yi a kan shugaban na Amurka wadanda aka yi satar fitar da su.

Kalaman batancin dai sun sa dangantakar da ke tsakanin gwamnatocin kasashen biyu ta dan yi tsami a ‘ayn kwanakin nan.

A wasu jerin sakonnin Tweeter da Trump din ya yi, ya ce daga yanzu ba zai kara wata mu’amulla da jakadan na Birtaniya ba, Sir Kim Darroch.

Shugaban ya bayyana hakan ne ‘yan sa’o’i bayan da Firaministar Birtaniyar Theresa May, ta yaba da jakadan, da cewa har yanzu tana da cikakken kwarin guiwa da yarda a kansa;

Jakadan na Birtaniya a Amurka ya caccaki gwamnatin Shugaba Trump inda ya bayyana ta da cewa, ta bankaura ce, mai rauni kuma wadda ba ta dace ba.

Hakkin mallakar hoto
PA Media

Image caption

A takardun sirrin, Sir Kim Darroch ya ce gwamnatin Trump ta bankaura ce kawai

A takardar diflomasiyya ta sirri wadda aka yi satar fitar da ita wadda Sir Kim Darroch, ya rubuta a ciki ya ce fadar gwamnatin Amurka, karkashin Trump ta sukurkuce tare da rarrabuwa.

Jakadan ya kuma bayyana gwamnatin ta Trump da cewa, ta bankaura ce, mai rauni kuma wadda ba ta dace ba.

Kan wadannan kalamai ne a yanzu shugaban na Amurka ya mayar da martani, tare da nuna rashin jin dadinsa ta Twitter, inda ya bayyana cewa yana fatan ganin an yi sauyi, a sama, wato dai sun raba gari da jakadan, yana neman da a janye shi daga Washington.

Ya ce shi bai ma san wannan jakada ba, kuma ko ma ya yake, ba a sonsa a Amurka, Ya kara da cewa a sakon nasa na Twitter, ”ba za mu sake yin wata harka da shi ba.”

Shugaban ya kuma ce, Theresa May ta yi shirme a shirin Birtaniya na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, sai dai ya ce, babban abin jin dadin shi ne, nan ba da jimawa ba, Birtaniya za ta samu sabon Firaminista.

Tun da farko kafin martanin na Trump, Mrs May da kuma ma’aikatar harkokin wajen Birtaniyar sun bayyana kwarin guiwarsu a kan jakadan, amma kuma sun nesanta kansu daga ra’ayinsa.

Sir Kim dai ya yi zama na arziki da gwamnatin ta Trump, sannan kuma ya yi aiki tukuru na ganin cewa an samu nasarar ziyarar baya-bayan nan ta shugaban na Amurka a Birtaniya.

A wani sakon na Tweeter Mista Trump ya ce ya ji dadin wannan ziyara ainun, amma ya ce Sarauniya ce ta fi burge shi.

Facebook Comments

Arewa

Kaduna: An kubutar da babban dan sanda daga hannun masu satar mutane

Published

on

Wani dan sandan Najeriya

Image caption

‘Yan sanda a jihar Kaduna, Najeriya, sun ce an yi nasarar kubutar da babban jami’in dan sandan nan da aka sace, ACP I. Musa, mai lakabin Rambo, a kan hanyar Kaduna zuwa Jos a karshen mako.

Mai magana da yawun rundunar DSP Yakubu Sabo ya ce an kubutar da babban dan sandan ne tare da direbansa ba tare da ko rauni ba.

Sai dai a tattaunawar da ya yi da BBC kakakin ya ki bayyana yadda aka yi nasarar kubutar da mutanen biyu, illa dai ya ce sai a nan gaba ne za su yi wannan bayani.

Game da cewa ko an yi wani dauki-ba-dadi da wadanda suka sace jami’an ‘yan sandan biyu,

ganin yadda a cikin dan lokaci da sace su har aka yi nasarar ceto su,

musamman ma a yadda ake ganin masu satar jama’a na da makamai, sai ya danganta hakan da irin kokarin jami’an tsaro.

Hakkin mallakar hoto
Inpho

DSP Sabo ya ce ba a wannan lokacin ba ne kadai aka taba yin irin wannan nasara ta saurin ceto wasu da aka sace cikin gaggawa ba.

Ya ce abu ne da ya dogara da yanayin aiki, wani lokacin a samu nasara da wuri wani lokacin kuma yakan dauki lokaci.

Game da yadda ake ganin ‘yan bindiga na yawan satar mutane da kai hare-hare a jihar ta Kaduna,

a matsayin wata alama ta tabarbarewar tsaro a jihar, mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce abin ba haka yake ba, domin ba kasar da ba a aikata laifuka.

Ya ce sai dai kawai idan abu ya yi yawa yana tayar da hankalin mutane, wanda kuma rundunar ta yin duk abin da ya kamata domin maganin matsalar.

Ya kara da cewa sakamakon irin matakan da suke dauka a yanzu ba a yawan satar mutane a titin Kaduna zuwa Abuja, da sauran hare-hare da ake kai wa jama’a a jihar.

Ya ce yawanci ma a yanzu masu aikata irin wadannan laifuka sun koma wasu jihohi da ke makwabtaka da Kaduna ne, inda ya bayar da misalin iyakar jihar da Nasarawa ya ce a yanzu wasu a irin wadancan yankuna da ke da iyaka da Kaduna ake laifukan.

Sai dai ya ce akwai bukatar sauran jihohi masu makwabtaka da Kaduna su hada hannu domin maganin matsalar.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Sabon salon hana satar amsa ya yanjo rudani a kasar Indiya

Published

on

ANI

Hakkin mallakar hoto
ANI

Wani jami’in wata makaranta a Indiya ya bayar da hakuri, bayan da wasu hotuna na wasu dalibai da suka rufe kawunansu da kwalaye yayin jarabawa ya rinka yawo a shafukan sada zumunta.

An dauki hoton ne a lokacin wata jarabawa a wata makarantar sharar fagen shiga jami’a ta Haveri da ke jihar Karnataka a Indiya.

Hotunan sun nuna daliban makarantar zaune a cikin aji da kwalaye bisa kawunansu, an huda kwalayen ta yadda za su samu iska.

An bayyana cewa an yi hakane domin hana daliban satar amsa.

Daya daga cikin malaman makaranatar ya fito ya roki gafara bayan afkuwar lamarin.

Ya ce makarantar ta yi amfani da wannan sabon tsarin ne sakamakon ta ji labarin tsarin ya yi amfani matuka a wata makarantar.

Ya kuma bayyana cewa an yi hakan ne da yardar daliban, kuma wasu daliban ma daga gidajensu suka zo da kwalayensu.

Ya ce ”ba a tilasta wa kowane dalibi da cewa dole sa ya saka kwali a kai ba, idan za ku iya gani akwai wadanda babu kwalin a kansu .”

Hakkin mallakar hoto
ANI

Ya ce ”wasu sun cire kwalayen bayan mintuna 15 wasu kuma bayan mintuna 20, bayan sa’a daya mu da kanmu muka ce kowa ya cire kwalin.”

Rahotanni sun bayyana cewa jami’ai a yankin sun garzaya makarantar bayan sun samu labarin wannan sabon tsarin da makarantar ta bullo da shi.

SC Peerjade wanda jami’i ne a kasar ya bayyana wannan sabon tsarin da makarantar ta yi gwaji a matsayin ”rashin imani.”

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

Amaechi ya duba sabbin jiragen kasa da za a kawo Najeriya daga China – AREWA News

Published

on

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya kai ziyarar gani da ido kamfanin dake aikin samarwa da Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya sabbin taragon jiragen kasa.

Amaechi wanda aka gwadawa jiragen ya yabawa kamfanin kan yadda suka kammala aikin akan lokaci.

Ya ce cikin watanni biyu masu zuwa jiragen za su iso Najeriya.

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited