Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) na tsawon shekara biyar.
Naɗin nasa zai fara aiki ne da zarar Majalisar Dattijan ƙasar ta amince da shi.
Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, yau Juma’a.
Bayanin ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne bisa dogaro da sashe na 8 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007, wadda ta bai wa shugaban ƙasar karfin ikon naɗa shugaba da mataimaka huɗu na Babban Bankin.
Sanarwar ta kuma bayyana sunayen wasu mutane huɗu da shugaban ya amince da su domin naɗawa a matsayin mataimakan gwamnan babban bankin na Najeriya.