Tinubu ya gana da ƴan wasan Super Eagles a fadar shugaban ƙasa

Shugaba Bola Tinubu ya gana da kungiyar Super Eagles a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ku tuna cewa Super Eagles ta sha kashi da ci 2-1 a hannun mai masaukin baki Ivory Coast a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 (AFCON) a daren Lahadi.

Bayan kammala wasan, shugaba Tinubu ya jinjina wa Super Eagles bisa jajircewar da suka nuna a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar.

Wasu rahotannin sun ce shugaban ya karrama ƴan wasan ne da lambobin yabo.

More from this stream

Recomended