Sudan: Za a saki daruruwan masu zanga-zanga

SUDAN PROTESTERS
Hakkin mallakar hoto
APF

Hukumomi a Sudan sun bayar da umarnin a saki dukkan wadanda ake tsare da su saboda zanga-zangar da suka fara a watan Disambar 2018.

Kunguyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam sun ce ana tsare da fiye da mutum dubu daya yayin da gwamnatin kasar ke kokarin kawo karshen zanga zangar kawo karshen mulkin Shugaba Omar el Bashir na tsawon shekara talatin.

Rahotanni na cewa an kashe fiye da mutum 40.

Ma’aikatar watsa labarai ta Sudan ta ce umarnin sakin wadanda ake tsare da su ta fito ne daga shugaban hukumar tsaro da leken asiri na kasar Salah Ghosh.

Akwai jagororin ‘yan adawa, da masu rajin kare hakkin dan Adam da ‘yan jarida cikin fiye da mutum 1,000 cikin wadanda ake tsare da su tun bayan da aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnati makonni shida da suka gabata.

Amma abu ne mai kamar wuya cewa wannan matakin zai sauya wa masu adawa da Shugaba Omar el Bashir ra’ayi akan kiraye-kirayen da suke yi na ya sauka daga mukaminsa.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

A yayin da matsalar tattalin arzikin kasar ke kara shiga halin hawula’u, da kuma hasashen cewa shugaban zai so ya sake tsayawa takara a shekara mai zuwa, fusatar da ‘yan kasar ke yi kan lamarin sai karuwa ya ke yi.

Abin dubawa a nan shi ne yadda jami’an tsaron kasar za su tunkari masu zanga-zanga a makonni da watanni masu zuwa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...