Connect with us

Hausa

Sudan: Malaman jami’a sun fara zanga-zanga

Men in a pickup truck

Hakkin mallakar hoto
Protester

Jami’an tsaro a Sudan suna tsare da wasu malaman jami’a da suka fito zanga-zanga a Khartoum, babban birnin kasar.

Likitoci da dama sun fito suna zanga-zanga a asibitoci inda suke kira da shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa, kuma tun watan Disambar bara jama’ar kasar ke karawa da jami’an tsaro.

Kungiyar Human Rights Watch mai fafutukar kare hakkin bil Adama ta ce jami’an tsaro sun kashe akalla mutum 50.

Ba kamar yadda aka saba gani a wasu sassa na nahiyar Afirka ba – inda yawancin masu fita zanga-zangar adawa da gwamnati kan kasance matasa marasa aikin yi ne.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Omar al-Bashir ya mulki Sudan tun 1989

Amma a Sudan likitoci maza da mata da malaman makaranta da sauran ma’aikata ne ke fuskantar harsasai da hayaki mai sa hawaye da kuma kulakan ‘yan sandan gwamnatin Shugaba Omar al Bashir.

‘Yan sa’o’i kadan da suka gabata an kame wasu malaman jami’a a birnin Khartoum.

An kuma gabatar da wasu jerin zanga-zanga a asibitoci goma cikin babban birnin kasar – an kuma bukaci Shugaba Omar al Bashir ya sauka daga mukaminsa.

Mako biyu da ya gabata gwamnatin Sudan ta ce za ta saki dukkan wadanda ta damke sakamakon zanga-zangar da aka shafe fiye da wata biyu ana yi a fadin kasar.

Amma yawancin wadanda ke tsaren ba su sami ‘yancinsu ba.

Masu rajin kare hakkin dan Adam a Sudan na fargabar cewa gwamnati na iya kama su domin gwamnatin kasar na tsare da mutane masu yawa a wurare na sirri.

Suna kuma tsorn jami’an tsaron na iya gallaza masu azaba.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Me yasa ‘yan Najeriya ke son komawa Canada?

'Yan Najeriya suna bayyana ra'ayinsu game da zaben 2019

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu ‘yan Najeriya suna bayyana ra’ayinsu game da zaben 2019

Wasu ‘yan Najeriya na tafka muhawara bayan da wasunsu suka ce za su koma kasar Canada saboda daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da hukumar zaben kasar ta yi.

Suna tafka muhawarar ne a shafin sada zumunta na Twitter.

Ba a san wanda ya fara amfani da maudu’in ba, sai dai a halin da yake ciki shi ne maudu’i mafi shahara a shafin Twitter a kan zaben Najeriya wadda hukumar zabe ta Najeriya ta daga zuwa makon gobe.

Maudu’in na cewa saboda fusatar da ‘yan Najeriya suka yi da matakin na hukumar zaben, shi yasa za su fice daga kasar zuwa Canada.

Amma wasu ‘yan Najeriyar na kallon batun ta fuskar barkwanci, kuma sun rika wallafa hotunan da kan sa mutane dariya da nishadi.

Hakkin mallakar hoto
KOLA SULAIMON

Image caption

Shugaban hukumar zabe a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu

Ga wasu daga cikin sakonnin da aka wallafa a shafin na Twitter:

Ye of Canada (@blaisemaen) ya wallafa hoton Atiku Abubakar da tsohon dan takarar mukamin gwamnan jihar Osun da bai yi nasara ba.

Ya nuna kamar mutanen biyu na tattaunawa kan batun na komawa Canada, amma ya sauya masu sunaye, inda ya kira daya John, daya kuma ya kira shi Saki:

John: Abokina ba ka san abin da na gani ba da na isa Canada ba.

Saki: Me ya faru?

John: Sai naga ‘yan Najeriya a ko’ina.

Wani mai suna @PaultwinOkoye ya wallafa wani hoton na wasu jiragen sama masu tarin yawa na tashi daga filin jirgin sama:

Hoton ‘yan Najeriya da ke ficewa daga kasar zuwa Canada 😂😂😂🤣🤣🤣🤣🏃🏃🏃🏃🏃

Shi kuwa @laffbro ya wallafa wani hoton motar bas ta haya da wasu fasinjoji ke kokawar shiga cikinta har ta tagoginta:

Yayin da ‘yan Najeriya suka ji yaron mota na kiran fasinja su tabbata sun shiga motar zuwa Canada da canjinsu na naira 200! 😂😂😂

Shi ma @s_potentials ba a bar shi a baya ba, domin ya wallafa wannan hoton na kasa da sako mai cewa:

Yadda ‘yan Najeriya ke shirin ficewa zuwa Canada a bana.

Sai kuma @YoungSaeed da ya wallafa sakon wasu fasinjoji tare da kayansu a kusa da wata motar haya:

‘Yan Najeriya na barin kasarsu zuwa Canada.

A karshe kuma ga wannan mai suna @psalmuel__ wanda ya ce:

Ina sanar da ‘yan uwana ‘yan Najeriya cewa kuna daf da rasa ni ga kasa mai alamar ganyen maple, wato Canada!

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

Wasu ‘yan siyasa a Zamfara sun nuna jin dadinsu game da dage zabe

Wasu ‘yan jam’iyyar APC a jihar Zamfara, musamman magoya bayan bangaren ‘yan takarar gwamnan jihar Abdul’aziz Yari sun nuna farin cikinsu game da dage zaben Najeriya da aka yi.

Har ya zuwa daren jiya dai jam’iyyar ta APC a jihar bata san makomarta a zaben ba, sakamakon matsayar hukumar zabe na cewa jam’iyyar a jihar ba ta da ‘yan takara a zaben na bana, kuma bata bada wata sanarwar warware matsayar ba, kwatsam sai ga sanarwar dage zabe.

Sai dai a bangare daya, duk da yake ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar da suke ta murnar matsayar hukumar zaben basu ji dadin dage zaben ba, suna ganin ba wani tasiri da hakan zai haifar.

To ko wannan ka iya kasancewa dama ga jam’iyyar APC a jihar ta samun shigar ‘yan takarar a zaben? Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya ce yana fatan hakan.

Da tsakiyar dare ne dai hukumar zaben Nigeria ta bada sanarwar dage babban zaben kasar da mako daya, lamarin da ya sa al’amuran yau da kullum suka dawo tamkar yadda aka saba a babban birnin jihar.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

2019: PDP ta yi martani dangane da dage zaben Najeriya

Shugaban jam’iyar PDP a jihar Adamawa Barr. A.T Shehu, ya bayyana cewa akwai lauje cikin nadi a wannan lamarin ganin yanayin da aka dage baban zaben da aka shirya yi yau asabar.

Shima dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, yace nan bada jimawa ba, zasu gana da masu ruwa da tsaki don fitar da matsaya, kan dage zabe, amma shi ma ya nuna bacin ransa.

Tuni wasu ma’aikatan wucin gadi da aka dauka don gudanar da aikin zaben suka nuna bacin ransu, musamman wadanda aka tura yankuna masu nisa.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: