Sojojin Najeriya Sun Kai Wa ‘Yan Boko Haram Mummunan Hari A Baga

Wannan da ba shi ne karon farko da sojin ke sake kwato Baga daga mayakan Boko Haram ba

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@HQNigerianArmy

Image caption

Wannan da ba shi ne karon farko da sojin ke sake kwato Baga daga mayakan Boko Haram ba

Rundunar sojan Najeriya ta sanar da cewa ta fattaki mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai wa dakarun kasashen yankin tafkin Chadi mai hedikwata a Baga hari a ‘yan makwannin da suka gabata.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce wasu dakarun kundumbala na sojojin Najeriya sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram bangare da ya yi mubaya’a ga kungiyar IS mai da’awar kafa daular musulunci da dama, a harin.

Mazauna yankin na Baga dai sun ce mayakan na Boko Haram da suka yi mubaya’a ga kungiyar da ke da’awar kafa daular musulunci a yammacin Afirk ke iko da garin na Baga.

To sai dai rundunar sojan Najeriya ta musanta cewa garin yana hannun Boko Haram.

  • Rundunar Sojin Najeriya za ta kwashe mutane daga Baga
  • Sojoji sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga

Sanrawar da Janar da daraktan yada labaran rundunar Janaral Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce, sojojin na musamman sun kuma kakkabe ‘yan Boko Haram daga wasu garuruwa da ke kan hanya, kamar Kukawa da Gudumbali da Kuros Kauwa, har ma ta samu nasarar kwato wasu makamai.

Sanarwar na nuna cewa a yanzu dakarun kasar ne ke da iko da Garin Baga, domin kuwa tuni dakarun na musamman suka hade da sojojin da ke Baga, wadanda suka fatattaki ‘yan Boko Haram.

Sai dai sanarwar ta ce an kashe sojoji biyu yayin fafatawar, sannan wasu biyar kuma sun jikkata.

Gagarumin aikin na hadin gwiwa ne tsakanin sojojin kasa da na sama da kuma na ruwa.

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@HQNigerianArmy

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...