Sojojin Najeriya sun kama wasu fitattun masu garkuwa da mutane guda biyu, Bashir Mohammed da Ismail Mohammad, a Jihar Filato.
Rundunar sojin ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook a ranar Lahadi, tana mai cewa jami’anta na Runduna ta 3 da ke karkashin Operation Safe Haven ne suka aiwatar da samamen.
A cewar sanarwar, an kai farmakin ne a ranar Asabar bisa ga sahihan bayanan sirri da aka samu.
“An gudanar da aikin ne a karkashin Operation LAFIYAN JAMA’A, inda aka kai farmaki a mafakar masu garkuwa da mutane da ke Katume High Grounds a karamar hukumar Bassa, bayan samun sahihan bayanai cewa masu garkuwa da mutane na boye wadanda suka sace a wurin yayin da suke neman kudin fansa,” in ji rundunar sojin.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa an kwato makamai masu hadari daga hannun miyagun, ciki har da bindigar AK-47 guda daya da kuma gidan harsashin bindiga guda daya.
“Masu garkuwa da mutanen da aka kama suna hannun jami’an tsaro, inda suke bayar da bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wajen cafke sauran ‘yan tawagarsu da kuma kwato karin makamai,” in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta jaddada cewa wannan nasara na nuna yadda Operation SAFE HAVEN ke aiki tukuru wajen yaki da rashin tsaro a yankin.
Sojojin Najeriya Sun Cafke Ƙasurguman ‘Yan Fashi Biyu a Jihar Filato
