Connect with us

Hausa

Sojoji sun mamaye kamfanin jaridar Daily Trust gida da waje

Published

on

Daily Trust

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK / DAILY TRUST

Sojoji da jami’an tsaro na cikin gida DSS sun mamaye ofisoshin kamfanin jaridar Daily Trust a Abuja da Maiduguri.

A lokacin da wakilin BBC ya isa ofishin a Abuja, ya taras da sojojin da kuma wasu jami’an tsaro sanye da farin kaya sun zagaye ofishin inda suka hana shige da fice.

Mataimakin babban editan jaridar Mahmud Jega ya fada ma BBC cewa sojojin sun isa ofishin da kimanin karfe 4 na yamma, kuma sun kutsa ciki da karfe 5.33.

“Sojoji sun rufe ofishinmu na Maiduguri da safiyar yau, kuma sun tafi da wasu ma’aikatanmu biyu. A halin yanzu suna tsare da su a can”.

Daga nan sojojin sun bukaci dukkan ma’aikatan su taru a wuri guda kuma sun gudanar da bincike akan ma’aikatan da ke cikin ofis.

Binciken da wakilin BBC ya gabatar ya tabbatar da sojojin sun kai wa jaridar ta Daily Trust wannan samamen ne saboda babban labarin da ta wallafa yau Lahadi a shafinta na farko.

“Sun bukaci dukkan ma’aikatanmu su fice daga harabar ofishin, kuma sun kwace dukkan na’urorin aiki a hannun ma’aiakatan namu”, inji Mahmud Jega.

Har lokacin da ake hada wannan rahoton sojojin na cikin harabar ginin kuma sun kashe wutar ginin baki daya.

Facebook Comments
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Hausa

Ina Neymar, Eriksen, Varane, Vorm, Mustafi, Ibe, Bravo za su tafi? | BBC Sport

Published

on

Neymar

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Juventus ta fara farautar Neymar

Barcelona na shirin karbar aron Neymar mai shekara 27 daga Paris St-Germain a wannan makon da nufin sayen dan wasan idan an sake bude kasuwar musayar ‘yan wasa. (ESPN)

Juventus ta shiga sahun manyan kungiyoyin da ke bukatar Neymar, inda ta fara tattaunawa da PSG domin karbar dan wasan na Brazil. (AS)

Barcelona ba ta shirya yin watsi da burin dawo da Neymar ba a Camp Nou. (Marca).

PSG ta fi son ta ba Real Madrid Neymar don ta karbi dan wasan baya na Faransa Raphael Varane, mai shekara 26, da kuma matashin dan wasa Vinicius Jr. (Telefoot, via Sun)

Dan wasan Tottenham na Denmark Christian Eriksen, mai shekara 27, ya ce yana sha’awar komawa Barcelona ko Real Madrid ko Juventus. (ESPN)

Arsenal za ta bar dan wasan Jamus Shkodran Mustafi, mai shekara 27 ya koma Roma a matsayin dan wasan aro amma da nufin sayar da shi kan fam miliyan £23m. (Forza Roma, via Sun)

Golan Chile Claudio Bravo, mai shekara 36 zai bar Manchester City a karshen kaka. (Sun)

Ole Gunnar Solskjaer ya nanata cewa Paul Pogba, mai shekara 26, ba zai bar Manchester United ba. (Sky Sports)

Facebook Comments
Continue Reading

Buhari

Tsokacin masana game da kalaman Buhari a taron ministoci

Published

on

Fadar shugaban Najeriya ta shirya taron sanin makamar aiki ga sabbin ministoci da shugaban ya nada domin gudanar da gwamnati a zango na biyu.

Yanzu haka masu fashin baki a fannin siyasar Najeriya na tsokaci game da kalaman da shugaban kasar ya yi a lokacin da ya gabatar da jawabi a wurin taron sanin makamar aikin ga asabbin ministocin da ya nada.

Batutuwan da shugaban na Najeriya ya tabo, a wurin taron, sun hada da bitar nasarorin zangon farko na gwamnatinsa da kalubalen yawan jama’a da Najeriya ke fuskanta da mafarkin gwamnatinsa na aza tubalin fitar da matalauta miliyan 100 daga kangin fatara cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban ya kuma tabo batun bukatar da ke akwai ga sabbin ministocin su hada hannu wuri guda ta fuskar tsarawa da aiwatar da manufofin cimma burin gwamnati a ma’aikatun da za su jagoranta.

Sai dai masu kula da lamura sun yi tsokaci game da lafuzzan shugaban.

Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata, shugaban kungiyar CAJA masu rajin tabbatar da adalci kawar da rashawa da kuma alkinta dukiyar kasa, ya ce bayannan shugaban sun saka shakku a zukatan jama’ar kasar.

Ya kuma kara da cewa jawabin nasa ya nuna cewa ita gwamnati ba ta da shirin da za ta kai kasar ga inda ta ce za ta kai ta.

Shi ma masanin kimiyyar siyasa da harkokin dimokaradiya, ya yi tafsili game da kalaman na shugaba Buhari.

Malam Kabiru Sufi, malami ne a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano, ya kuma ce jama’a suna jiran su ga an fitar da wani daftari ko wani babban kudiri da ya wuce wanda aka fitar a halin yanzu.

Yanzu dai ‘yan Najeriya na dakon ganin kamun ludayin sabbin ministocin bayan shugaba Buhari ya tura su ma’aikatun da za su yi wani lokaci a nan gaba.

Facebook Comments
Continue Reading

Buhari

Najeriya za ta daukaka kara kan shari’arta da P&ID a Birtaniya

Published

on

Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
Buhari Sallau

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar kama wasu jami’ai da ta ke zargi da hannu a wani hukuncin kotun Birtaniya da ya bukaci sai ta biya wani kamfani tsabar kudi har dala biliyan 9, saboda saba yarjejeniya da suka kulla.

Wata kotun London ce ta umarci gwamnatin Nijeriya a ranar Juma’a ta biya kamfanin Process & Industrial Developments Ltd (P&ID) wadannan makudan kudi ta hanyar kwace kadarorinta.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya ce batun tsohuwar shari’ah ce da jami’an gwamnatocin baya suka gaza wajen daukaka kara, har damar ta rufe.

“Masu mulki a wancan zamani ba su daukaka kara ba har kofa ta tsoshe,” in ji shi.

Ya kuma ce gwamnatin Buhari ta yi kokarin tunanin matakin da za ta dauka don jinkirta aiwatar da hukuncin domin bude kofar ta daukaka kara amma kotun a Ingila ta ce ba zata bayar da wannan dama ba.

Ya zargi jami’an gwamnatin baya da yin sakaci kan abin da ya kira hadin bakinsu don a cuci Najeriya har suka bari abu ya kasance haka.

Ya ce duk da gwamnati za ta daukaka kara amma abu na farko da za a yi shi ne duk wani wanda aka san da hannunsa a cikin wannan hadin baki don a cuci Najeriya tare da wani kamfani na kasar waje, gwamnati za ta sa a kamo su kuma za ta dauki mataki akansu.

Wata sanarwa a shafin intanet na kamfanin ta ce yarjejeniyar ta ba shi damar gina wata katafariyar masana’ntar gina sarrafa iskar gas wadda Najeriya za ta karba kyauta don bunkasa lantarki a kasar.

Amma kamfanin ya ce ya fuskanci karin kudin ruwa a kullum saboda rushewar yarjejeniyar, batun da lauyoyin gwamnatin Najeriya suka ce ya wuce hankali.

Tun farko a 2017 kotu ta bukaci Najeriya ta biya kamfanin kusan dala biliyan shida da rabi kafin yanzu kuma kotun London ta kara dala biliyan biyu da miliyan dari hudu.

jimillar kudin dai ta kai kwatankwacin kashi 20 cikin 100 na dukiyar da Najeriya ta ce ta tara na lalitar kudadenta na kasashen ketare wato dala biliyan 45.

Facebook Comments
Continue Reading
Advertisement
Advertisement

Trending

%d bloggers like this: