Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane Biyu Daga Hannun Ƴan Fashin Daji A Sokoto

Dakarun rundunar sojan Najeriya dake aikin yaƙi da ƴan ta’adda a jihar Sokoto sun samu nasarar daƙile yunkurin yin garkuwa da mutane inda suka kashe ƴan ta’adda huɗu da kuma kuɓutar da wasu mutane biyu daga hannun ƴan ta’addan.

Sojojin sun samu nasara ne biyo bayan amsa kiran kai ɗaukin gaggawa da suka samu daga dajin Baniguntu da Gohanau dake ƙaramar hukumar Gudu inda suka yi mummunar musayar wuta da ƴan ta’addar inda suka kashe wasu kana wasu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Mutanen da aka ceto  Isya Nura da Salihu Hamza an miƙa su ga shugaban ƙaramar hukumar Gudu domin a duba lafiyarsu kana a miƙa su ga iyalansu.

Bindiga ƙirar AK-47 guda biyar da kuma harsashi 32 aka samu daga hannun

More from this stream

Recomended