A cigaba da ƙoƙarin da take na kakkaɓe sauran mayaƙan ƙungiyar IPOB dake fafutukar kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabashin Najeriya dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe da dama daga cikin mayakan a wani gurmuzu da suka yi da su.
Dakarun sojan na rundunar Operation UDO KA sun gudanar da aikin sintiri akan titin Ekeututu-Ihiteunansa dake ƙaramar hukumar Orlu ta jihar Imo.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce a lokacin sintirin dakarun suka yi arangama da wasu da suke zargin mayaƙan ƙungiyar ta IPOB ne. mayaƙan da dama ne suka mutu a yayin da wasu su ka tsere da raunin harbin bindiga a fafatawar da aka yi.
Har ila dakarun sun samu nasarar gano bama-bamai da kuma wasu kayayyaki da ake amfani da su wajen ƙera bam da kuma wasu guraye na tsafi.
Babban hafsan sojan ƙasa na Najeriya, Janaral OO Oluyede ya yabawa dakarun kar gwarzantakar a da suka nuna kana ya shawarce su da su ƙara kaimi wajen fatattakar ƴan ta’addar.