Sojoji sun kama mutane 8 masu kai wa ƴan ta’adda makamai da kayayyaki

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama wasu mutane 8 da ake zargi da samarwa ƴan ta’adda makamai da kuma safarar kayayyaki a jihohin Yobe da Taraba.

A wata sanarwa ranar Litinin rundunar ta ce dakarun sun kai farmaki wata maɓoya da ake zargin ta ƴan ta’adda ce a ƙauyukan Maraban Donga da kuma Munya dake karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.

Rundunar sojan ta ce an kai farmakin ne tare da haɗin gwiwa sauran hukumomin tsaro a ranar 30 ga watan Agusta.

Mutane biyar aka kama  a farmakin tare da gano bindiga ƙirar AK-47 guda uku, bindigogi biyu ƙirar gida, bindiga biyu ƙirar dobul barel, bindigar mafarauta guda biyu, harsashi 61 da kuma gidan zuba harsashi guda 8.

Sauran karin kayayyakin da aka gano sun haɗa da ankwar hannu guda ɗaya, wuƙar sojoji  uku, hular kwano ta ƴan sanda, gatari, na’urar POS da kuma wayoyin hannu 10.

Har ila yau rundunar sojan ta ce  mutane uku dake kaiwa mayaƙan Boko Haram kayayyaki aka kama a ƙauyen Jimbal dake ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen sun shafe shekaru suna gudanar da wannan sana’ar inda suke kaucewa jami’an tsaro ta hanyar haɗa baki da ƴan bijilante.

Kayan da aka gano a wurinsu sun haɗa da motoci uku, baburan hawa biyar, tayoyin babur masu yawan gaske, bangarorin injin babur daban daban-daban da kuma magunguna masu yawa.

Sojojin sun kuma ƙwace dilar yadi da ƴan ta’addar ke amfani da shi wajen ɗinka kayan yunifom.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...