Sojoji sun hallaka ‘yan Boko Haram 39 a Tafkin Chadi – MNJTF

Sojojin Najeriya

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/@HQNIGERIANARMY


Rundunar hadakar ta kunshi kasashen yankin Tafkin Chadi

Rundunar hadaka ta dakarun kasashe da ke yaki da ‘yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi, MNJTF ta ce ta yi nasarar hallaka, ‘yan kungiyar 39 tare da kwace musu makamai a wani dauki-ba-dadi, Cross Kaura da ke jihar Borno.

Dakarun na hadakar kasashen da ke yaki da mayakan kungiyar ta Boko Haram a yankin na Tafkin Chadi, sun ce reshe ne ya juye da mujiya a wannan dauki ba dadi.

Kasancewar masu tayar da kayar bayan na Boko Haram ne suka kai musu wani hari a yankin, amma sai zaratan sojojin hadakar wadanda ke zaman shiri suka mayar da martani, tare da karya lagon masu ikirarin Jihadin, kuma suka yi musu mummmunar illa.

A sanarwar da sojin hadakar, na Multi National Joint Task Force suka fitar mai dauke da sa hannun, kakakinsu Kanar Timothy Antiigha, sun ce a yayin wannan gumurzu da suka yi ranar Talata, a ci-gaba da aikin da suke yi a wannan yanki, da aka yi wa lakabi da Yancin Tafki, sun yi nasarar, hallaka mayakn Boko Haram 39 tare kuma da kwace makamai da dama.

A sanarwar dakarun sun ce sojinsu 20 wadanda suka ji rauni a yayin wannan bata-kashi, an debe su a jirgin sama inda aka fice da su daga wannan yanki domin a je a yi musu magani, kuma suna samun kulawa.

Harwayau, a wata sanarwar wadda ita kuma ta fito ne daga, rundunar sojojin sama na Najeriya, wadda ke dauke da sa hannun Darektanta na hulda da Jama’a Air Commodore Ibikunle, Daramola, rundunar ta ce, ta samu nasarar watsa gungun wasu ‘yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara.

Rundunar ta ce sakamakon rahotannin da ta samu cewa wasu gaggan mahara na tattaruwa a yankin kauyukan Rafi da Doka a Gundumar Mada da ke karamar hukumar Gusau, a jihar ta Zamafara, nan da nan rundunar ta tashi zaratanta na musamman a jiragen yaki, domin tarwatsa ‘yan bindigar daga garuruwan biyu, a ranar Talata kenan.

Sanarwar ta kara da cewa zuwan dakarun wuraren ke da wuya, sai suka hadu da tirjiya daga ‘yan bindigar, wadanda suka bude wa dakarun saman na musamman wuta, amma kuma ina sojin sun yi amfani da dabaru suka ci lagonsu.

A wannan dauki-ba-dadi sojin na najeriya suka ce sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga biyu, yayin da saura suka tsere da raunukan bindiga.

Sanarwar ta ce sojojin na sama da sauran takwarorinsu za su ci gaba da wannan aiki har sai sun raba maharan da yankin Arewa maso yamma na Najeriyar.

Sai dai kuma a dukkanin sanarwar biyu ta fafatawar biyu ta yankin na jihar Zamafra da kuma ta yankin na Tafkin Chadi ba wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...