Sojoji a birnin Ibadan  sun kama ƴan fafutukar kafa ƙasar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Masu fafutukar sanye da kayan sojoji na  ƙasar waje kuma ɗauke da makamai sun farma sakatariyar gwamnatin jihar Oyo dake birnin na Ibadan.

Ɓullar labarin ke da wuya sojoji suka garzaya wurin inda suka yi wa sakatariyar ƙawanya inda suka samu nasarar kama su bayan da suka nuna turjiya ta hanyar musayar wuta.

Ƴan fafutukar sun buƙaci a gaggauta fara shirin ɓallewar yankin daga Najeriya domin kafa ƙasar ta Oduduwa.

More from this stream

Recomended