Connect with us

Hausa

Singapore: An bayyana sunayen masu kanjamau 14,000 a intanet

Published

on

An bayyana cewa 'Yan sanda a kasar suna neman agaji daga kasashen ketare a kan wannan lamari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An bayyana cewa ‘yan sanda a kasar Singapore suna neman agaji daga kasashen ketare a kan wannan lamari
bayan an wallafa sunayen mutane kusan 14,000 masu dauke da cutar kanjamau (HIV) a shafin intanet a kasar.

Bayanan da aka wallafa na dauke da sunayen ‘yan kasar ta Singapore da baki mazauna kasar.

Sunayen dai wasu takardun sirri ne na kiwon lafiya da ake zargin wani Ba’amurke ne mai dauke da cutar ya sace sunayen ya wallafa.

Wannan kutsen yana zuwa ne watanni kadan bayan wani kutse da aka yi a intanet inda aka sace muhimman bayanai na mutum miliyan daya da rabi a kasar wanda ya hada da na Farai Ministan kasar Lee Hsien Loong.

Sunayen da aka wallafa dai na dauke da bayanai da suka hada da adireshin mutanen, bayanai a kan cutar da suke dauke da ita da sauran bayanai da suka shafi lafiyarsu.

Jami’ai a kasar sun bayyana cewa an kawo cikas ga bayanai a kan sunayen ‘yan kasar 5,400 da kuma baki mazauna kasar 8,800.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Mikhy Farrera-Brochez, wanda ake zargi da wallafa sunayen

Ko kun san wa ya wallafa sunayen?

Jami’an kasar dai sun bayyana wanda ya wallafa sunayen a matsayin wani Ba’amurke, mai hekara 31, mai suna Mikhy Farrera-Brochez wanda ya taba zama a kasar ta Singapore.

An taba daure Mista Mikhy sakamaon laifin da ya aikata na safarar miyagun kwayoyi da almundahana a shekarar 2016.

Mista Mikhy dai tsohon abokin aikin Ler Tech Siang ne wanda kuma shi ne tsohon shugaban sashen kiwon lafiya na kasar.

Shima Mista Siang an daure shi a kwanakin baya sakamakon taimaka wa Mista Mikhy da ya yi domin sauya bayanan lafiyarsa a kan cutar kanjamau domin ya samu damar shiga kasar.

Facebook Comments

Hausa

APCn Jihar Edo ta dakatar da Adams Oshiomole

Published

on

Oshiomole

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar

Jam’iyyar APC reshen jihar Edo ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Comrade Adams Oshiomole.

Shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 18 a jihar ne suka kada kuri’ar yanke kauna kan Adams Oshiomole a ranar Talata, kamar yadda shugaban jam’iyyar na jihar Aslem Ojezu ya shaida wa manema labarai.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamna Oshiomole da kuma mai-ci Godwin Obaseki suna kokawar neman iko ne da jam’iyyar a jihar ta Edo.

Sai dai Oshiomole bai ce komai ba game da dakatarwar, sannan kuma babu tabbas kan yadda hakan zai shafi aikace-aikacensa a matakin kasa a matsayinsa na shugabanta.

Rikicin ya samo asali ne tun daga watan Yuni lokacin da ‘yan majalisa tara cikin 24 na majalisar jihar suka zabi kakakin majalisar da sauran shugabanninta.

Za mu ci gaba da bin wannan labari domin kawo maku karin bayani da zarar mun samu.

Facebook Comments
Continue Reading

Arewa

An dakatar da ma’aikatan gwamnati 500 a jihar Adamawa

Published

on

Fintiri

Gwamnatin jihar Adamawa ta dakatar da wasu ma`aikatan Kwalejin fasahar jihar kusan mutum 500 daga aiki.

Gwamnatin dai ta ce ta sallame su ne saboda ba a bi ka`ida ba wajen daukarsu aiki.

Hakan na zuwa ne bayan da wani kwamitin da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya kafa ya gudanar da bincike, wanda a cikin rahotonsa ya gano kura-kurai a daukar da aka yi wa ma`aikatan.

To sai dai ma’aikatan da aka dakatar sun musanta batun rashin cika ka’ida wajen daukar tasu.

Wata malamar kwalejin da sallamar ta shafa ta ce rayuwarta ta gigita tun bayan dakatarwar.

“Na karbi takardar nan, ina fita ban san inda kaina yake ba kawai sai na fadi. Duniyar gaba daya ta fita daga kaina ban san mene ne yake yi min dadi ba.

“Wata bakwai ina aiki ba a biya na. Kuma an tantance ni, ba ni da wata matsala. Iyayena ba su da karfi sannan ga marayu a gabana.”

Gwamnatin dai ta yi zargin cewa wasu ma`aikatan ba su da cikakkiyar shaidar kammala karatu ko kwarewa, yayin da wasu kuma take zargin gwamnatin da ta gada ce ta gaggauta daukarsu aiki a lokacin da wa`adinta ke gab da cika.

Sai dai wasu daga cikin ma`aikatan da aka sallama, sun ce babu gaskiya a hanzarin da gwamnatin ke kawowa.

Hasali ma dakatarwar ta shafi wasu ma`aikatan da ke wasu ma`aikatun gwamnati.

Sai dai gwamnatin jihar Adamawa a nata bangaren, ta ce har yanzu ba ta yanke shawara a kan makomar sauran ma`aikatan da ba na kwalejin fasahar ba, wadanda aka dakatar da su, kasancewar kawo yanzu ba a mika mata cikakken rahoto a kan su ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri dai ya yi ikirarin kyautata rayuwar ma`aikata tun lokacin yakin neman zabe, abin da ke daure kai shi ne yadda gwamnatinsa ta fara sa kafar-wando guda da irin wadannan ma`aikata.

To sai dai da ma tun a lokacin da yake kaddamar da gwamnatinsa ya ce ba zai iya tafiya da ma`ikatan da gwamnatin da ya gada ta dauka aiki tana gab da shudewa ba.

Facebook Comments
Continue Reading

Hausa

United na shirin sayo Zaha, Man City za ta kashe makudan kudi

Published

on

Wilfried Zaha

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Manchester United na shirin fitar da kudi fan miliyan 70 domin sake sayo dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha, mai shekara 26, wanda ya kasance tare da su a tsakanin 2013 da 2015. (Sun)

Liverpool na shirin tattauna wa da dan wasan Scotland Ryan Fraser, mai shekara 25, daga Bournemouth a watan Janairu. (Talksport)

Tottenham ta shirya tayin tsohon dan wasan Lyon mai shekara 25, Memphis Depay, a kan kudi fan miliyan 50 wanda ya taka leda a Manchester United tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017. (Mirror)

Tsohon dan wasan Liverpool Xabi Alonso, mai shekara 37, da kocin Tottenham Mauricio Pochettino, mai shekara 47, na cikin jerin ‘yan takarar kujararar tsohon kocin Bayern Munich da aka kora Novac Kovic. (Star)

Rahotanni na cewa Manchester City na shirin kashe kudi kusan fam miliyan 100 a kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu, bayan da ta gaza kai bantanta a wasan da suka fafata da Liverpool a gasar Premier. (Mirror)

Rahotanni na cewa Manchester United ba ta da niyyar sayen tsohon dan wasan gabanta,Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, a watan Janairu. yayin da kwantiraginsa a LA Galaxy ya kusa karewa. (Sky Sports)

Golan Arsenal Gernd Leno, mai shekaru 27, da alama dai zai maye gurbin Manuel Neuer mai shekara 33 a Bayern Munich yayin da kungiyar ta kyalla ido a kan sa (Sun)

Borussia Dortmund har yanzu dai tana zawarcin dan wasan gaba na Everton Anthony Gordon, mai shekara 18, duk da an ki tayin dan wasan dan kasar Ingila. (Football Insider)

Za a bai wa kocin Arsenal Unai Emery dama a wasanni shida masu zuwa da kungiyar za ta yi domin tabbatar da cewa zai iya ci gaba da jagorantar kungiyar. (Standard)

Tsohon kocin Spain Luis Enrique, wanda ake ganin zai iya maye gurbin Emery a Arsenal, ba ya tunanin komawa kungiyar a yanzu. (ESPN)

Dan wasan Newcastle Matty Longstaff, mai shekara 19, zai rattaba hannu kan wata sabuwar kwantaragi a ‘yan makwanni masu zuwa sai dai an shaida wa dan uwansa mai shekaru 22, Sean ya nuna bajinta daga nan zuwa watanni 12 don samun sabuwar yarjejeniya. (Telegraph)

Dan wasan gaban Spain Ayoze Perez, mai shekara 26, ya bayyana cewa ya janye komawarsa Valencia daga Newcastle a lokacin bazara. (Mail)

Tottenham, Chelsea, Watford da Norwich sun shirya tayin dan wasan Metz Habib Diallo a watan Janairu. Dan wasan dan kasar Senegal mai shekara 24 ya zira kwallaye takwas a wasanni 13 da ya buga zuwa yanzu. (Teamtalk)

West Ham na duba yiyuwar sayen sabon mai tsaron raga a watan Janairu, bayan da kungiyar ta gaza tantance yanayin Roberto. Dan wasan dan kasar Spain, mai shekara 33 kwallaye 13 ya tare wa kungiyar a wasanni shida na Premier tun bayan da ya maye gurbin Lukasz Fabianski da ya tafi hutun jinya. (The Athletic – subscription required)

Kocin Hammers Manuel Pellegrini na kokarin samo mafitar da zai kare kansa bayan nasarar da suka samu a hannun Burnley. (Sun)

Facebook Comments
Continue Reading

Trending

© Copyright 2019 - AREWANG Media Limited