
Shugabannin kungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun amince su tattauna da mambobinsu bayan ganawar da suka yi da tawagar gwamnatin tarayya a ranar Laraba kan yajin aikin da ake yi.
Taron ganawar ya gudana ne a ofishin mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu dake Abuja domin lalubo mafita kan yajin aikin.
Ma’aikatan sun tsunduma yajin aiki a ranar 14 ga watan Nuwamba domin nuna rashin amincewarsu kan yadda aka ci zarafin Joe Ajaero shugaban kungiyar kwadago ta NLC a jihar Imo.
Kungiyar ta yi zargin cewa kawo yanzu babu wanda aka kama ballantana gurfanar da su gaban kotu kan batun.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar kan yajin aikin mai bawa shugaban ƙasar shawara kan sha’anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce tuni aka kama wasu da ake zargin suna da hannu kan lamarin.
Taron ganawar da aka yi ya samu halartar ministan ƙwadago Simon Lalong da kuma karamar ninistar ma’aikatar, Nkeiruka Onyeajeocha.
Da yake magana bayan zaman da aka yi shugaban kungiyar TUC ya ce sun tattauna sosai da tawagar gwamnatin tarayya.