Shugabannin kananan hukumomi 13 sun koma jam’iyyar PDP a jihar Benue

[ad_1]








Sha uku cikin shugabannin kananan hukumomin jihar Benue 17 da aka zaba karkashin jam’iyyar APC sun tsallaka ya zuwa jam’iyar PDP.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku bayan da gwamnan jihar Samuel Ortom ya shiga jam’iyar PDP.

Lokacin da yake sanarwar komawarsa jam’iyar PDP ranar Laraba a gidan gwamnatin jihar, Ortom ya ce dandazon magoya baya suna jiran su biyo shi sabuwar jam’iyar ta sa.

“Da nake magana daku yanzu 10 cikin yan majalisa 17 na jam’iyar APC suna son biyo ni sabuwar jam’iyar,”ya ce.

Jumullar shugabannin kananan hukumomi 13 da kuma kansiloli 276 ne suka halarci taron da ya gudana a sabon dakin taro na gidan gwamnatin jihar dake Makurdi.

A yanzu dai jam’iyar PDP ce babbar jam’iya a jihar inda take da sanatoci biyu, shugabannin kananan hukumomi 13 da kuma gwamnan jiha




[ad_2]

More News

Ɗalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...