Shin ka san wane ne marigayi Justice Mamman Nasir?

FACEBOOK/AMINU GAMAWA

Hakkin mallakar hoto
FACEBOOK/AMINU GAMAWA

An haifi Justice Mamman Nasir a jihar Katsina a shekarar 1929.

Ya yi karatun sakandare dinsa a Kwalejin Kaduna inda ya samu takardar shaidar kammala karanun sakandare ta WAEC a 1947.

Daga bisani ya tafi jami’ar Ibadan inda ya samu digiri a harshen Latin.

Daga nan kuma ya tafi makarantar horar da lauyoyi inda ya samu digiri a bangaren shari’a a 1956 kuma a wannan shekarar ce aka rantsar da shi a matsayin cikakken lauya a wata kotu da ke Ingila da ake yi wa lakabi da ‘Licoln Inn.”

Ya dawo Najeriya a 1956 a matsayin lauya mai shigar da kara.

A 1961, an nada shi Ministan Shari’a na Arewacin Najeriya inda ya shafe shekaru biyar kan mukamin sai kuma daga baya ya zama darakta a ofishin lauyoyi masu shigar da kara na arewacin Najeriya a 1967.

A 1967 din dai Mamman Nasir ya zama babban lauya a ma’aikatar shari’a a jihar arewa ta tsakiya a wancan lokaci.

Ya rike wannan mukamin na shekaru bakwai inda daga nan ne aka nada shi alkalin kotun koli a 1975.

An kuma nada shi a matsayin shugaban kotun daukaka kara, mukamin da ya rike kenan har zuwa 1992 inda daga nan ne ya zama Galadiman Katsina.

An nada shi a matsayin Galadiman Katsina a ranar 9 ga watan Mayun 19992.

Ya kuma rasu ranar Asabar 13 ga watan Afrailun 2019.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Wani mutumi ya kashe mahaifiyarsa a kan kudi

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mazaunin kauyen Kajola da ke kusa da Apomu a jihar mai suna Lukman Adejoju bisa...

Mayaƙan Boko Haram Biyu Sun Miƙa Kansu Ga Sojoji

Rundunar dakarun soja ta ƙasa da ƙasa wato Multi National Task Force(MNJTF) a turance shiya ta 3 dake Monguno a Najeriya ta bayar da...

Sojoji a birnin Ibadan  sun kama Æ´an fafutukar kafa Æ™asar Oduduwa

Dakarun rundunar sojan Najeriya  sun samu nasarar kama wasu mutane masu fafutukar kafa ƙasar Oduduwa a birnin Ibadan na jihar Oyo. Masu fafutukar sanye da...